CORONAVIRUS: Najeriya ta haramta jekala-jekala da mai cutar daga wannan jiha zuwa waccan

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa daga yanzu duk jihar da aka samu wani dauke da cutar Coronavirus, to a wannan jihar za a killace shi har sai ya warke.

Wannan kenan ana nufin an hana daukar wani mai dauke da cutar daga wata jiha a maida shi jihar sa ta haihuwa, kamar yadda aka a faru aka dauki wani daga Kano zuwa Jigawa.

Wannan bayani ya na kunshe cikin yarjejeniyar da aka cimma a Taron Majalisar Kolin Kiwon Lafiya, wanda Ministan Lafiya ya jagoranta, tare da Kwamishinonin Lafiya na kowace jiha, tare da Sakataren Kiwon Lafiya na FCT, Abuja.

Da ya ke magana ranar Laraba, Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ya ce daukar matakin ya zama wajibi, domin a dakile fantsamar cutar Coronavirus a cikin jihohin kasar nan.

“Duk wanda aka samu da cutar Coronavirus a wata jiha, to a wannan jihar za a killace shi, a kula da shi, ba sai an dauke shi zuwa jihar sa ta asali ba.”

Idan ba a manta ba, an samu takun-saka tsakanin jihohin Kano da Jigawa, yayin da Kano ta maida wa Jigawa wani mai dauke da cutar Coronavirus.

Haka nan kuma tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, an dauke shi daga Abuja zuwa Lagos domin neman magani.

Sannan kuma bayan rasuwar sa an yi ta jagainiyar daukar sa zuwa Abuja.

Ehanire ya ce an kafa Tsarin Dauka Da Zirga-zirgar Mai Dauke Da Coronavirus a Abuja, kuma za a kafa irin wannan tsarin a kowace jiha.

Ya ce akwai jirage mallakar Rundunar Sojojin Sama da Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa wadanda aka kebe domin jigilar majiyyacin da ke cikin matsanancin halin da tilas sai an dauke shi zuwa wurin da za a fi kulawa da shi, fiye da inda ya ke a killace.

A kullum sai karin masu dauke da cutar a ke samu a Najeriya. Haka kuma duk da ana samun wadanda ke warkewa, an bada rahoton mutuwar mutum 25 a Najeriya.

Share.

game da Author