CORONAVIRUS: Sanata Barau ya roki Buhari ya ceci al’ummar Kano

0

Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin daga Kano, ya roki Shugaba Muhammadu Buhari ya taimaka wa Jihar Kano da kudaden da za a yi amfani da su, domin a magance masifar cutar Coronavirus.

Cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja, Barau Jibrin, wanda shu ke wakiltar Kano ta Arewa, ya ce akwai bukatar Gwamnatin Tarayya ta kai wa Kano daukin dakile cutar wadda a yanzu ta ke kara fantsama a Kano, inda ake matukar bukatar kayan aiki da kayan gwaji da sauran su.

Barau ya ce idan aka ceto Kano tamkar an ceto Arewa ce ko ma kasar baki daya, idan aka yi la’akari da yawan al’ummar da ke jihar da kuma irin tasirin da Kano ke da shi, a Arewa da kasa baki daya.

Ya zuwa ranar 22 Ga Afrilu, akwai mutum 73 da suka kamu a jihar Kano.

Sanatan ya tunatar da Gwamnatin Tarayya yadda ta kwashi makudan kudade ta bai sa jihar Lagos domin ta yaki cutar Coronavirus.

Sanatan ya kara da cewa alkaluman kididdiga na nuni da cewa jihar Kano aka fi yawan kamuwa a yanzu idan aka cire Lagos. Don haka, tunda babu jihar da za ta iya yakar wannan cutar ita kadai, wajibin gwamnatin tarayya ne ta gaggauta kai wa Kano tallafi, tun kafin abin ya gagare ta.

Haka nan kuma Barau Jibrin ya jinjina wa irin kakarin daukar matakan da Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi wajen saurin tashi tsaye ya kafa wasu tsauraran matakan hana cutar fantsama sosai tun da farko.

Ya ce shi kan sa Shugaban Hukumar Kula da Cututtuka ta Kasa, NCDC Chikwe Ikpeazu ya jinjina wa Gwamna Ganduje.

Sai dai kuma a Kano ana fama da mace-mace, wadanda yawancin jama’a ke ganin cewa ana fama da wata cutar mai kashe mutane fiye ma da Coronavirus.

Share.

game da Author