Mahaifin tsohon gwamnan Barno, Ali Modu Sheriff, Galadima Sheriff ya rasu a safiyar Alhamis.
Galadima Sheriff ya rasu a gobara da ya afka wa gidan sa dake Maiduguri a safiyar ranar Alhamis.
Mutane sun yi ta aikawa da salon ta’aziyyan su ga iyalan marigayin.
Kakakin gwamnan jihar Barno, Isa Gusau, ya mika ta’aziyyar sa ga iyalan Marigayi Galadima Sheriff da mutanen jihar Barno.
Gusau ya ce wannan babban rashi ne ga Mutane da jihar baki daya. Ya Kara da cewa Galadima yayi mutuwar shahada kamar yadda addinin musulunci ya karantar.
” Mutum na biyu kenan da yayi mutuwar shahada a jihar Barno. Na farko dai, Abba Kyari me, da ya rasu cikin annoba, sai kuma Galadima Sheriff da ya rasu a cikin gobara.
Gusau ya Yi addu’ar Allah ya jikan mamatan.
Idan ba a manta ba, gwamnatin jihar Barno ta garkame jihar na kwana 14 domin dakile yaduwar cutar coronavirus a Jihar.