CORONAVIRUS: Masari ya soke dokar hana Sallar Juma’a, ya ce a daina doguwar huduba

0

Yayin da Gwamnatin Tarayya ke ta hakilon jan-hankali, wayar da kai da kuma tirsasa a daina cakuduwa wuri daya, domin gudun kamuwa da cutar Coronavirus, shi kuma Gwamnan Katsina Aminu Masari, ya dade dokar dakatar da sallar jam’i wadda da kan sa ya sa wa hannu a makon da ya gabata.

Jihar Katsina ta sa dokar hana cakuduwa wuri daya, ciki har da dakatar da sallar Juma’a tun a makon da ya gabata.

Sai dai kuma ba zato ba tsammani a ranar Talata sai ga takardar sanarwa an fitar, mai dauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Mustapha Inuwa, ya na mai cewa:

“Sakamakon wani taro da Gwamnatin Jihar Katsina ta yi da limamai, sarakunan gargajiya da kuma jami’an tsaro, ana sanar da janye dokar dakatar da sallar jam’i ba tare da bata lokaci ba.”

Sanarwar ta yi kira ga dukkan limaman masallatan Juma’a su tabbatar sun gudanar da sallar Juma’a a bisa tsarin kiyaye kamuwa da annobar Coronavirus da gwamnati ta ke kira a rika kiyayewa.

Sannan kuma ya roki jama’a a yi kaffa-kaffa daga cakuduwa da juna.

Yadda Masari Ya Ce A Yi Sallar Juma’a A Katsina

Cikin sanarwar wadda Sakataren Gwamnati Inuwa ya sa wa hannu, an umarci limamai kada wanda ya yi doguwar huduba. A gaggauta yin sallah, a sallame kowa ya kama gaban sa, domin gudun daukar cutar Coronavirus a tsakanin masallatan a junan su.

Sannan kuma an ja hankalin mamu cewa kada a cakudu da juna, a yi nesa-nesa da juna, abin da za a iya cewa na nufin ko da sahu ya hadu, to kada a hada kafafu da kafadar juna.

Juma’ar da ta gabata an hana yin sallah a Katsina. Har jami’an tsaro suka kama wani limami da ya yi sallar Juma’a.

Kama limamin ya fusata matasa har suka yi dandazo, suka kone wani ofishin ‘yan sanda.

Share.

game da Author