Facebook zai takaita aika sakonni ta WhatsApp, saboda masu tura labaran karrairayi kan Coronavirus

0

Masu watsa labarai na rudu, bogi da karairayi ta WhatsApp sun ka wa sauran jama’a fushin kamfanin Facebook.

Facebook, wanda shi ke da hakkin mallakar kafar sadarwa ta soshiyal midiya, WhatsApp, ya sanar cewa zai rage yawan sakonnin da kowane mai amfani da WhatsApp ke turawa, domin dakile baza labaran karairayi da bogi a duniya kan Coronavirus.

Wannan tsatstsauran mataki kuwa ya biyo bayan zargin da aka yi cewa an yi amfani da WhatsApp ne wajen watsa labarai na kazafi, kage, sharri da bogi cewa rumbun babbar datar intanet mafi girma a duniya, wato 5G, ita ce ta haddasa cutar Coronavirus.

Wannan rudu da ji-ta-jita da ya game duniya, ya shiga kunnen milyoyin jama’a musamman matasa, wadanda suka yi imani ko amanna cewa 5G ne ya haddasa Coronavirus a duniya.

Hakan kuwa ya tunzira matasa masu yawan gaske a Ingila, har su ka ragargaza rumbunan 5G sama da 20 a Ingila.

“Mun yi amanna cewa idan aka tsaurara matakai, to za a rage matukar masu yada karairayi ta WhatsApp masu yawan gaske a kan Coronavirus.

“Don haka mu na sanar da cewa za mu takaita aika sakonni ga mutane da yawa ta WhatsApp. Idan aka turo maka sako, to mutum daya tal za ka iya tura wa salon kadai.

Matsalar da ke tattare da WhatsApp, ita ce masu kamfanin ba su iya ganin sakonnin da masu amfani da WhatsApp ke turawa a wurare birjik.

Ba kamar Facebook da ke iya ganin duk abin wani ya tura. WhatsApp ya na tattara tattara bayanai da dama da kuma saukin turawa ga dimbin jama’a a duniya.

Sannan kuma akwai dubnan gurup-gurup na sa da zumunta a duniya.

Cutar Coronavirus na ci gaba da yi wa dimbin jama’a mummunan kisa a duniya, bayan ta kama sama da mutum milyan daya.

Share.

game da Author