Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ya bayyana cewa an dakatar da gwajin masu cutar Coronavirus a Kano ne saboda wasu masu gwajin sun kamu da cutar a dakin da su ke yin gwajin.
Ehanire, wanda ya yi wannan bayanin da yammacin Ladaba, ya ce an kuma fuskanci karancin sinadarai da kayan aikin gwajin, wanda hakan ya sa tilas aka dakatar na wani dan takaitaccen lokaci.
“Rahotanni sun tabbatar an samu karancin kayan aiki musamman kayan kariyar da jami’an kiwon lafiya ke sakawa da daurawa. Kuma an samu karancin wasu sinadarai. Amma dai a yanzu duk mun tura musu kayan.
” Wasu masu aikin gwajin sun kamu a dakin da ke yin gwajin. Hakan ya sa tilas aka gaggauta rufe dakin gwajin, daga baya aka je aka yi masa feshin tsarkakewa daga. cutar Coronavirus.”
Ehanire ya ce rufewar ta wani dan takaitaccen lokaci ce, kuma tuni an ci gaba da aikin gwajin, saboda an aika musu da dukkan kayan aikin da ake bukata.
PREMIUM TIMES ya tabbatar da cewa ana a cikin Asibitin Koyarwa na Aminu Kano ake gwajin a wani dakin gwajin cututtuka (laboratory).
Can ne kuma ake kai gwaje-gwaje ana aunawa da jihohin Arewacin kasar nan da dama.
Jihar Kano ce ta uku a jerin jihohin kasar nan da suke fama da cutar coronavirus.