HukumarLafiya ta Duniya (WHO), ta nuna matukar damuwa dangane da yadda wasu kasashe ke ta hankoron janye dokar zaman gida domin hana fantsamar cutar Coronavirus.
Babban Daraktan WHO, Tedros Ghebreyesus ne yayi wannan bayani a lokacin da ya ke jawabi tare da yin gargadin cewa a daina gaggawar janye dokar a kasashe daban-daban.
Coronavirus ta kashe sama da mutum 100,000 a duniya kuma akalla sama da mutum milyan biyu a duniya.
Shugaban na WHO ya ce ya na fargaba cewa matsawar wasu kasashe suka gaggauta janye dokar, to za a iya fuskantar cutar ta sake danno kai a cikin kasashen da suka janye dokar ta zaman gida.
“Duk da cewa Coronavirus ta dsn you sauki a kasashen Turai din da a baya suka fi ko’ina fama da cutar kamar Spain, Italy, Jamus da Faransa, to amma kuma ta na kara kamari a Afrika da Amurka sosai.
“Kenan a irin wadannan kasashe yin gaggawa ta cire dokar killace kai a gida ka iya sake haifar da fantsamar cutar a cikin jama’a.
A Najeriya Shugaba Muhammadu Buhari ya yi jawabin a ci gaba da zaman gida tare da kiyaye bin ka’idojin da jami’an lafiya suka gindaya.
Har yau dai masana kimiyya da sauran likitoci na duniya ba su gano maganin cutar Coronavirus ba.
Cutar ta tsaida harkokin hada-hada manya da kanana tsaye cak a fadin duniya. Farashin danyen mai ya karye, daga dala 57 zuwa har kasa da dala 19.
Matsalar ta haifar da gagarimar matsala a Najeriya, inda har ta shafi kasafin kudin kasar.
Gwamnatin Tarayya na ci gaba da bayar da tallafin kudade da kayan abinci ga marasa galihu. Sai dai kuma shirin rabon tallafin na shan suka daga dimbin dimbin jama’a, su na ganin cewa ana karkatar da kudaden ta wata hanya daban.
Discussion about this post