Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya roki ‘yan Najeriya su ci gaba da hakuri a zauna a gida. Buhari ya bayyana cewa hakan shine zai taimaka wa kasa Najeriya waje aikin dakile yaduwar cutar coronavirus da ya ke yaduwa kamar wutan daji a duniya.
Buhari ya roki mutane su daure da zaman gida zuwa wani lokaci.
“A yau mun fahimci cewa akwai ‘ya’yan da sun kasa ziyartar iyayen su, kuma akwai dattawan da aka raba su da matasa ko kanana da dama. Akwai kuwa wadanda a rayuwa sun dogara ne sai sun fita yau su ke samun na cin yau ki na gobe, masu fuskantar tantagaryar kuncin wahala
“Babu wata Gwamnatin Dimokradiyya da ke yawan rokon wadanda su ka zabe ta kamar yadda a yau mu ke rokon ku. Duk duk da yawan rokon ku da mu ke yi, za mu dai sake rokon na ku da ku daure ku ci gaba da bin umarnin zaman gida a dukkan wuraren da aka bayar da wannan umarni. To a takaita zirga-zirga. A bi dokokin da masana kimiyyar mu da likitocin mu suka gindaya mana. Wato a ci gaba da zaman gida. A rika wanke hannuwa domin a ceci rayuka.
“Ga wadanda ke kara shiga halin kuncin rayuwa, Gwamnatin Tarayya ta kara kaimin ci gaba da talllafawa da kayan agaji. An kara fitar da tan 70,000 na kayan abinci daga Rumbun Ajiyar Abinci na Kasa domin rabawa ga wadanda suka shiga cikin matsanancin halin kunci. Sannan kuma za a ci gaba da raba tallafin kudaden da ake kan rabawa a dukkan jibohin kasar nan da kowace karamar hukuma.
“Mu na kira da mu rika zaman sauraren sanarwa daga kafafen yada labarai dangane da yadda yadda yadda yadda a rika karbar wadannan kaya da kudaden agaji. Ta haka za ku ma kara fahimtar irin tallafin da za a kara bayarwa nan gaba.
“Mu na rokon ku kara kuma ku ci gaba da jure wannan mataki tsatstsaura da ake dauka, ba don komai ba, saboda duk duniya har yanzu babu inda aka samu magani, rigakafi ko makarin wannan cuta. Yanzu kenan zabi ya rage na mu, ko dai mu bada kai bori ya hau, ko kuma mu ci gaba da fuskantar zaman takura ta hanyar kiyayewa da bin ka’idoji a cikin kunci domin mu samu mu rabu da wannan cuta.
“To amma a wannan mawuyacin hali da ake ciki. Hakkin mu ne mu bayyana mu ku hakikanin gaskiyar lamari: Kasashen duniya 210 su na faman yadda yadda za su rabu da wannan annoba da ta zama alakakai a fadin duniya. Saboda haka kowace kasa ta-kan-ta ta ke yi. Babu wata kasa da za ta zo ta taimake mu. Sai dai mu tashi mu taimaki kan mu mu kori wannan cuta daga kasar mu da kan mu.
“Ashe kenan mu ne da kan mu za mu fatattaki wanann cuta daga kasar mu da kan mu. Bai yiwuwa mu zauna jiran sai wasu sun shigo sun taimake mu. Babu tsimi babu dabara, sai dai mu taimaki kan mu da kan mu kawai, mu dakile wannan annoba daga cikin mu. Kuma tilas hakan za mu yi. Kuma za mu iya, idan mu ka hada hannu a matsayin mu na ‘yan Najeriya.”