Coronavirus ta dira Jihar Kano, Yanzu 318 a Najeriya

0

Jihar Kano ta samu nata rabon na yaduwar cutar coronavirus a Najeriya inda aka samu mutum na farko ya kamu da cutar.

Bayanai sun nuna cewa wannan mutumin da ya kamu da cutar ya tattago ta ne daga birnin Abuja. Yanzu haka yana killace a wurin da aka tanada domin wadanda za su kamu da cutar a jihar.

Hukumar NCDC ta sanar cewa akalla mutum 13 ne suka kamu da cutar a sakamakon gwajin ranar Asabar. 11 daga Legas, 1 daga Kano 1 daga jihar Delta.

Mutm 70 ne suka warke zuwa yanzu sannan mutum 10 sun rasu.

Yanzu an atbbatar da yaduwar cutar zuwa jihohi 19 kenan banda Abuja.

Lagos- 174
FCT- 56
Osun- 20
Edo- 12
Oyo- 11
Ogun- 7
Bauchi- 6
Kaduna- 6
Akwa Ibom- 5
Katsina-4
Delta- 3
Enugu- 2
Ekiti- 2
Rivers-2
Kwara- 2
Ondo- 2
Benue- 1
Niger- 1
Anambra- 1
Kano-1

Jihar Kano ce jiha ta uku a yankin Arewa maso Yamma da cutar ta bayyana. Jihar Kaduna ce ta farko, da take da mutum 6 da suka kamu zuwa yanzu, sai Jihar Katsina 3, sai kuma yanzu jihar Kano.

Share.

game da Author