Uwargidan Bill Gates, Melinda ta bayyana damuwar ta cewa ya kamata kasashen Afrika su tashi tsaye, su sake shiri, kada cutar Coronavirus ta yi musu irin fantsama da buwayar da ta yi wa kasashen Turai, Amurka da kuma China.
Da ta ke tattauawa a gidan talbijin na CNN, a kan illar Coronavirus a kasashe masu tasowa, Melinda ta ce wato idan cutar ta yi mummunar barkewa a Afrika, to za ta yi mummunar barna a dukkan kasashe masu tasowa.
“Ai ni da na ga irin yadda cutar ke barna da kisa, farkon abin da ya O min shi ne kasashen Afrika. Domin abin tausayawa ne. Na su da ingancin kiwon lafiya, kamar manyan kasashen duniya, wadanda cutar ta nukurkusar. To ina ga ta barke a can kuma?!
“A bar ganin wai cutar ba ta kutsa Afrika ko kasashe masu tasowa sosai ba. Ni ina ganin dalilin da ya sa babu cutar a can a yanzu sosai, saboda ba su da kayan gwaji wadatattu, kamar manyan kasashe.”
Ta ce idan za a karade jama’a ana gwaji, to za a yi mamakin sakamakon da za a gani.
Melinda ta ce, “ai da na ga yadda a kasar Equador ake fito da gawarwaki daga cikin gidaje ana jibgewa bakin titina, hankali na ya tashi. Na tuna irin lungunan garuruwan Afrika da na shiga har cikin matsugunan marasa galihu.
“Su irin wadannan mutanen, idan ma ka ce Slsu zauna a gida, ko kuma ka ce su rika wanke hannaye, duo abu ne mai wahala a wurin su.”
Daga nan ta yi kira ga manyan hukumomin bayar da agaji cewa kada su karaya, akwai bukatar a ci gaba da tallafawa ga kasashen nahiyar Afrika.