Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, kuma Dan takarar shugaban kasa na zaben 2019 a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa cutar Coronavirus ta kama dan sa.
Ya yi wannan jawabi a ahafin sa na tweeter da kan sa a ranar Lahadi da dare, misalin karfe 11.
“Ina mai sanarwa cewa an gwada da na kuma an tabbatar da ya na dauke da cutar Coronavirus. Tuni aka gaggauta sanar da Cibiyar Kula da Cututtuka ta Kasa, wadanda suka garzayo suka dauke shi. Yanzu haka an killace shi a Cibiyar Killace masu cutar Coronavirus da ke Gwagwalada, Abuja.
” Ina rokon a wannan mawuyacin halin da ake ciki, za ku sa dan nawa a cikin addu’a. Tare da kara jaddada muku cewa cutar Coronavirus gaskiya ce.”
Atiku dai bai bayyana sunan dan na sa da ya ce ya kamu ba.
Wannan ya kai ga lissafin wadanda suka kamu da cutar a Najeriya sun kai 28 kenan, wadanda 19 daga cikin su a Jihar Lagos ne.
Har yau dai babu rahoton wanda cutar ta kashe a Najeriya. Sannan kuma mutane biyu ne aka tabbatar da warkewar su, kuma tuni aka sallame su.
Gwamnati na ta kokarin bin-diddigin zakulo duk wasu da ake tunanin sun yi mu’amalar kusanci da wadanda suka kama da cutar domin a gwada su, ko kuma a killace su.
Zuwa ranar Lahadi Coronavirus ta kashe mutane 13, 071 a duniya, yayin da mutum 311,796 ne suka kamu. Mutum 95,838 kuma sun warke, an sallame su.