Hukumar NCDC ta sanar da bayyanan wasu mutane uku da suka kamu da cutar.
Hukumar ta ce wadannan mutane da suka kamu, duk sun shigo Najeriya daga kasashen waje me, banda mutum daya da ya kamu ta hanyar mu’amula da wani da ya kamu cutar.
Daya daga cikin wanda ya shigo da cutar daga Amurka, ya shigo Najeriya tun makonni 6 da suka wuce amma sai yanzu aka gano yana dauke da cutar.
Dayan kuma ya shigo Shima da ita me daga kasashen waje.
Zuwa yanzu wadanda suka kamu a Najeriya sun kai akalla mutane 30 sannan biyu sun warke.
Dukkan su suna killace a asibiti ana duba su.
1 – A rika Wanke hannuwa da sabulu a duk lokacin da aka dan wataya ko kuma aka yi tabe-taben abubuwa. Ko bako Kayi ka bashi dama ya wanke hannu kafin ku fara mu’amala.
2 – Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da gefen Hannu amma ba da tafin hannu ba. Idan kun shafi bakunan ku toh, ku wanke hannu maza-maza.
3 – A daina taba idanuwa da hannaye ko kuma hanci da baki. Ka du rika yawan shafa fuskokinku da hannaye. Idana an yi haka a gaggauta wanke hannaye.
4 – A nisanci duk wani da bashi da lafiya, musamman mai yin Mura da tari. Ko zazzabi ne yake yi a nisanta da shi sannan a bashi magani da wuri. Idan abin ya faskara a gaggauta kaishi asibiti domin a duba shi.
5 – A kula da yara sannan a rika tsaftace muhalli.
6 – A rika gaisawa da juna nesa-nesa
7 – Idan kayi bako daga kasar waje, kada a kusance shi koda dan uwana ne sai ya killace kan sa na tsawon makonni biyu.
8 – A rika Karantar da yara yadda za su kiyaye koda an aike su a waje.
9 – A yawaita cin abinci masu gina jiki, shan ruwa da motsa jiki.
10 – A yawaita yin addu’a da sadaka.
Discussion about this post