Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa muddin Kotun Koli ta kwace zaben Jihar Zamfara daga PDP ta bai wa APC, to ita ma PDP za ta sake maka wasu zabukan da aka yi a baya a Kotun Koli, wadanda ta ke ganin cewa an tafka mata magudi a lokacin.
Kakakin Yada Labarai na PDP, Kola Ologbandiyon ne ya bayyana wa manema labarai haka, a ranar Lahadi a Abuja, a yayin wani taron manema labarai da ya kira.
Ya ce ‘yan Najeriya sun hakura, kuma sun gamsu da matsayar da Kotun Koli ta dauka a kan wasu kararrakin da ta bibiya, inda ta ce ba ta da hurumin soke wani hukunci da ta rigaya ta yanke a baya.
Kotun Koli dai ta ce ana ta iya sake maida tsohon gwamnan Imo, Emeka Ihedioha da na Bayelsa a kan mukaman su.
A kan haka ne PDP ta ce ita ma ta gamsu da haka. Don haka ba za ta zura ido ta kyale Kotun Koli ta kwace Jihar Zamfara daga PDP ba.
“Idan har Kotun Koli ta sake duba shari’ar zaben Jihar Zamfara, to PDP ba ta da wani zabi, sai ita ma ta sake garzayawa kotu domin ta nemi a sake wasu shari’u na wasu zabuka da mu ke ganin ba a yi mana adalci ba.”
Idan za a tuna, Kotun Koli ta hana jam’iyyar APC shiga zaben gwamna a Jihar Zamfara. Da farko dau Kotun Daukaka Kara ta amince su shiga zabe, bayan Babbar Kotun Tarayya ta hana.
Bayan kammala zabe kuma sai Kotun Kolu ta tsaya kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya, inda ta kwace nasarar zabukan daga ga hannun APC ta damka wa PDP.