BIDIYON TSIRAICI: Deezell ya maka Maryam Booth a Kotu, yana neman ta biya miliyan 10

0

Fitaccen mawaki Ibrahim Rufai, da aka fi sani da Deezell ya maka Maryam Booth a Kotu.

Ba ita kawai ba Deezell ya hada da wasu su biyar a karar da suka hada Maryam Aliyu Obaje, Sarki @waspapping, Imam Anas, Auwal Fulani da @UnscramZ.

Idan ba a manta ba Deezell ya umarci Maryam Booth da ta janye wann zargin cewa shine ya saka bidiyon ta tsirara a shafukan Soshiya Midiya.

Maryam ta zargi Deezell wanda tsohon saurayinta ne kamar yadda ta bayyana cewa shine ya dauke tsirara sannan ta ce lallai za ta garzaya kotu bayan ta kamala bincike akai.

Sai dai kuma mawaki Deezell ya bayyana cewa ba zai taba yin irin haka ba ganin cewa shi musulmi ne da yake kiyaye dokokin Allah.

Sannan ya umarce Booth ta rubuta masa shimfidaddiyar wasikar tuba da janye wannan korafi na ta akan shi.

Da bata yi haka ba sai Deezell ya shigar da kara a kotun Abuja ya na bukatar Maryam ta biya shi naira miliyan 10 kan abinda ta yi masa.

Har yanzu dai Maryam bata ce komai akai ba. Sai dai tuni kotu ta mika wa wadanda aka maka su gabatanta sammacin bayyana a kotu.

Wannan cakwakiya dai ta jirkita farfajiyar Kannywood inda masoya da abokanan aikin Maryam suka rika fitowa suna nuna rashin jin dadin su ga abin da ya faru da jarumar.

Da yawa basu ji dadin yadda aka yada wannan bidiyo na Maryam ta na tsirara ba a wani daki da yayi kama da Otel.

Share.

game da Author