Jigon APC na neman diyyar naira bilyan 4 daga wata jarida

0

Wani jigo na jam’iyyar APC mai suna Nasiru Danu, rubuta wa mawallafin jaridar intanet, ta ‘Point Blank News, Jackson Ude wasika, inda ya nemi ya biya shi diyyar naira bilyan 4 saboda ya bata masa suna.

Ya ce Point Blank News ta buga labarin kage da bogi a kan sa, wanda kwata-kwata ba gaskiya ba ne.

Ya ce an kirkiri labarin ne da gangan domin kawai a bata masa suna.

A cikinn wasikar, lauyoyin Danu, wanda dan kasuwa ne, sun nemi a cire labarin daga ‘shafukan soshiyal midiya’ ciki har da twitter.

Sun bayyana cewa wannan labari ya zubar wa Danu kima da mutuncin sa a cikin jama’a. Kuma sun ce girman Danu ya fadi warwas daga idon masu ganin sa da kima.

Wani babban lauya mai suna Bode Olanipekun ya sawa wasikar hannu, kuma ya jero wasu rubuce-rubuce ko labarai da ya ce Point Black ta rika bugawa don bata sunan Danu.

Wasikar ta lissafo wurare har bakwai da ta ce sau bakwai Point Blank na bata sunan wanda suke karewa, wato Danu.

Ranar 20 Ga Fabrairu, jaridar ta buga cewa Danu da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari sun raba dala milyan 2 da suka wasga daga harkallar kwangilar odar kananan kwale-kwale ga sojojin Najeriya.

Sun dai bai wa Point Blank kwanaki bakwai ta biya kudin kuma ta cire labarin, ko kuma a maka ta kotu.

Share.

game da Author