Za a kara kudin wutar lantarki zuwa kashi 35% bisa 100% -Jami’in Gwamnati

0

Wani jami’in Hukumar Watar Lantarki ya bayyana cewa ‘yan Najeriya ba da dadewa ba za su fuskaci Karin kudin wutar lantarki har kashi 35 bisa 100.

Kenan wutar da maigida ke sha ta naira 10,000 za ta koma naira 13,500.

Ya yi wannan furuci ne ga manema abarai a Abuja, shugabannin gudanarwar kamfanin raba wutar antarki na AEDC, ya ce hukumar kula da wutar lantarki ta kasa ta fara kokarin gyara fasashi da saisaita adadin fasashin mitar wuta, zuwa sabon fasashin iya-kudin-ka-iya-hasken-wutar-ka.

Ije Okeke ya bayyana cewa, “mu na kokarin yin Karin kamar kasha 35 bisa 100 na farashin kudin wutar lantarki.”

AEDC ta ce ta shirya taron ne domin wayar wa jama’a kai dangane da laifin da ake dora mata a ko da yaushe idan batun matsalar wuta ya taso.

Kamfanin ya ce su iyar adadin wutar da gwamnati ta ba su, to da shi suke amfani.

Ya kara da cewa kusan kashi 60 bisa 100 na wutar da suke rabawa ba a samun kudin shiga daga masu amfana.

A yanzu dai ‘yan Najeriya na biyan naira 24 duk kilowatt daya na wutar lantarki. Idan aka fara amfani da farashin Karin, zai kasance duk kilowatt daya zai koma naira 32 kenan.

Ana dai ganin wannan Karin kudin wutar lantarki zai kara harzuwa mafi yawan ‘yan Najeriya wadanda ke amfani da tsarin biyan kudin ‘yar-canke, wanda ba a amfani da mita.

Duk da dai ba a san ranar da za a fara amfani da wannan sabon tsarin karin kudin wutar lantarki ba a Abuja da sauran wurare, amma dai ita gwamnatin tarayya ta aza ranar 1 Ga Afrilu za ta fara amfani da Karin kudin wutar lantarkin a kan ‘Yan Najeriya.

Duk da an shafe shekara da shekaru ana kasha wa bangaren hasken lantarki makudan bilyoyin nairori, har yanzu karfin wutar lantarkin Najeriya ba ta wuce migawatts 5000 ba.

Sannan kuma migawatts 1,750 kadai ake iya samarwa a kowace rana.

Shugaban kamfanin AEDC, Eanest Mupwayo, ya yi maraba da hana kamfanoni raba wutar da ta wuce naira 1,800, ba tare da an bai wa kwastoman mita ba.

Sai dai kuma ya ce matsalar wutar lantarki ta wuce batun wa ya mallaki mita ko wane ne bai mallaki mita ba.

Mupwayo ya kara da cewa bankunan kasuwanci sun ki bai wa masu kamfanonin raba hasken wutar lantarki ba shi domin su yi odar mita masu yawa a daga waje.

Ya ce dala milyan 150 da aka kebe domin sayo mitoci, kokadan ba za su isa ko su wadatar ba.

Sama da shekara biyar kenan tun bayan sayar da kamfanin wutar lantarki, NEPA, har yau milyoyin ‘yan Najeriya ba su da mita.

Share.

game da Author