Hukumar Kula da Kadarorin Najeriya (AMCON), ta kwace gidan da tsohon makusancin Shugaba Muhammadu Buhari, Buba Galadima ke ciki.
Ta kuma kwace ginin sa da kamfanin sa mai suna Bedko Nigeria Ltd ke ciki da kuma kamfanin gaba dayan sa.
Kwace kadarorin na Buba Galadima a yau Talata a Abuja, ya biyo bayan wani sammaci da Hukumar AMCON ta ce ta samo na iznin kwace kadarorin daga Babbar Kotun Tarayya a Abuja.
Kakakin AMCON, Jude Nwauzor ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya bayar a Abuja.
Ya ce Mai Shari’a A.I Chikere ne ya bada sammacin umarnin kwace kadarorin na Galadima.
Ya ce an kwace kadarorin ne bayan da kamfanin Buba Galadima ya kasa biyan bashin naira bilyan 900 da ake bin sa, wanda ya karba a Bankin Unity.
Ya ce an tsara yarjejeniyar biyan kudaden tun cikin 2011, amma bai biya ba.
Galadima na daya daga cikin makusantan Buhari na kut-da-kut tun daga lokacin da Buhari ya fara fafutikar shiga siyasa da neman zama shugaban kasa, har zuwa 2015.
Ya yi Sakataren Jam’iyyar APC na Kasa, jam’iyyar da Buhari ya tsaya takarar a karkashin ta a zaben 2011.
Galadima na daya daga cikin mutane 9 da suka sa hannun amincewa da yin gambizar hadewar jam’iyyun da suka haifar ko suka kafa APC.
Wakilin PREMIUM TIMES HAUSA ya garzaya gidan na Buba Galadima da ke Lamba 4, Titin Bangui, a Wuse 2, Abuja, inda ya samu jami’an tsaro na ‘yan sanda da dama da kuma jami’an AMCON sun a kokarin lallai sai Galadima ya kwashe kayan sa a lokacin nan take, ya fice daga gidan.
Ya samu zantawa da shi, inda ya karyata AMCON, kuma ya ce bi-ta-da-kulli ne kawai ake yi masa, saboda ya matsa wa Shugaba Buhari da caccaka da kuma gaskiyar da ya ke fadi.
Ya ce, “Don ka karbi kudi da nufin yin odar takin zamani a cikin 2003, ka aika ta kudin a bankin Amurka, sai aka rike kudin, jami’an Amurka suka ce su na binciken bankin da aikata wani laifi, kuma har yau ba a maido maka kudin ka ba, to mene ne laifi na.
“Da farko an kai ni kara kotu, na yi bayani, da na ga ana neman a yi min kulle-kulle, sai na daukaka kara.
“Na daukaka kara, kuma kotu ta gamsu, an kori karar. Yanzu kuma daga baya an zo ana musguna min, ana wulakanta ni saboda siyasa. To ni dai ba zan daina fadin gaskiya ba.” Inji Galadima.
Galadima yace shi ma har yanzu jiran a maido masa da kudin ya ke yi.
A lokacin da wakilin mu ke gidan, ya bar Galadima ya fito a kofar gida zaune, ya na jiran motocin da za su je su kwashe kayan sa daga cikin gidan.
Tun bayan raba hanya da aka yi da Buba da kuma Buhari, ya fice daga APC ya ke sukar gwamnatin Buhari.
A Zaben 2019 ya yi Daraktan Kamfen na dan takarar PDP, Atiku Abubakar.
Galadima ya yi ikirarin cewa an yi wa Atiku magudi, sannan kuma ya kalubanci Buhari ya rantse da Alkur’ani cewa ba shi da masaniyar an yi magudi.
Yanzu haka akwai ‘yar sa da ke aiki a karkashin gwamnatin Buhari, wadda Buharin ne madaurin auren ta, a lokacin da ta yi aure ‘yan shekaru baya.
An kuma yi cacukui da shi a lokacin zaben 2019, ba a sake shi ba sai bayan kammala zabe.