FALLASA: Yadda aka kulla wa Obasanjo da ‘Yar-Adua sharrin yunkurin kifar da gwamnatin Abacha -Farida Waziri

0

Tsohuwar Shugabar EFCC, Farida Waziri, ta fito a karon farko ta bayyana yadda aka kitsa tuggu da sharrin da aka kulla wa wasu manyan kasar nan cewa wai sun shirya kifar da gwamnatin marigayi Sani Abacha, a cikin shekarar 1995.

Wadanda ta bayyana karara cewa sharri aka yi musu, sun hada da tsohon shugaban kasa na mulkin soja a lokacin, Olusegun Obasanjo, sai mataimakin sa Shehu ‘Yar’Adua da Kanar Lawan Gwadabe da babbar ‘yar jarida, Chris Anyawu.

Farida, wadda ta na cikin lauyoyin da aka sa aiki tare da Kwamitin Bincike na Musamman, ta yi wannan bayani ne dalla-dalla a cikin wani littafin ta wanda zai fito kwanan nan, mai suna ‘Farida Waziri: One Step Ahead.’

Ta ce gaba daya duk karya ce da sharri da kullalliya da tuggu kutunguilar masu mulki a kan wasu manyan da ke adawa da tsarin su. Amma babu wani juyin mulkin da aka yi yunkurin shiryawa.

Abacha ya yi mulki daga ranar 17 Ga Nuwamba, 1993 zuwa watan Yuni, 1998. Ya daure su Obasanjo da ‘Yar’adua rai da rai, bayan rokon sa da aka yi ta faman yi cewa Kasa ya kashe su.

Yayin da ‘Yar’Adua ya mutu a kurkuku, an rage wa Obasanjo shekarun dauri zuwa 30, daga bisani kuma 15.

Yar’Adua ya rasu a kurkukun Abakaliki a ranar 8 Ga Disamba, 1997, bayan an rage masa wa’adin dauri zuwa shekaru 25.

Obasanjo ya shafe shekara 3 a tsare a kurkukun Gashuwa. Da Abdulsalami ya haura mulki duk ya saki wadanda aka daure. Bayan siyasa ta dawo shekara mai zuwa, Obasanjo ya zama shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP.

‘Yadda Aka Kitsa wa Yardua Sharri

Farida ta bayyana yadda wanda ya makala sunan ‘Yar’Adua a cikin masu yunkurin juyin mulki, ya kasa bayar da hujja ko da guda daya tal.

“Misali, ya ce sun je wurin Yar’Adua a gidan sa Ikoyi, sun yi mitin. Amma masu bincike sun dauke shi a mota, ya kasa gane gidan.

“An kuma kewaya da shi, amma ya kasa gane ko da wani gini ko bishiyar da ke kan hanyar zuwa gidan ‘Yar’Adua.

“A karshe kuma an tabbatar karya ya ke yi, da ya ce sun kuma taba yin mitin da ‘Yar’Adua, kamar su 50 a gidan sa.

“A karshe da aka dauke shi aka kai shi gidan Yar’Adua din, an ga cewa falon gidan duk yadda za a cusa mutane, ba zai wuce ya dauki mutum 20 ba. Amma shi kuma ya ce au 50.

“Da aka kure ramin karyar sa, sai ya ce a gaskiya wani jami’in SSS ne ya ba shi wata takarda mai dauke da bayanan yadda zai fadi rawar da Shehu ya taka a yunkurin juyin mulkin.”

“An umarce shi ya kone takardun idan ya gama kulla wa Yar’Adua sharri. Amma dai mun gano su a cikin silin rufin dakin sa.” Inji Farida.

Farida ta ci gaba da bayar da labarin irin halin da ta ga ‘Yar’Adua, lokacin da ake gabatar da shi a gaban su.

“A ranar farko bayan an shigo da shi, aka ajiye shi a daki, amma akwai glashi a tsakanin mu. Sai na lura ya rika zukar taba sigari, ba kakkautawa. Da wannan ta mutu, sai ya kunna wata, ko hutawa ba ya yi.

“Kuma na lura ya na sha, ya na taro, amma bai daina ba. Sai na tashi na je wurin sa, na ce: ” Ranka ya dade, ka daina shan sigarin nan mana. Ai ta na yi maka illa a lafiyar ka.

“Sai ya ce min, ” to idan ke ce ki ka tsinci kan ki a wannan yanayin, me za ki yi? Na ce masa Yallabai idan ni ce, addu’o’i kawai zan rika yi.”

A karshe dai daga mu lauyoyi har masu bincike, muka yi matsaya cewa ‘Yar’Adua ba shi cikin masu juyin mulki, amma ya na da masaniya, sai dai bai sanar ba. Aka zarge shi da laifin boye abin da ya san zai faru da gwamnati kawai.

Sharri Kayan Kwalba

“Babban abin da ya ba ni haushi da bacin rai da takaici, washegari mu na komawa gidan da ake zaman sauraron bincike a Ikoyi, Lagos, sai na samu masu bincike sun sauya zargin da ake wa ‘Yar’Adua zuwa ‘cin amanar kasa.’

“Hankali na kuwa ya tashi, na kalle su, na ce ya za Ku yi haka? Ai ba haka mu ka amince ba. Daga nan na daga fayil din da ke a hannu na, na buga shi a kan tebur, na fice, na nufi gida.

“Na samu miji na Ajuji, na shaida masa abin da aka shirya wa ‘Yar’Adua a wurin bincike. Sai ce min ya yi ni ma na yi kaffa-kaffa.

“Na je Hedikwatar mu ta ‘Yan Sanda, na samu Sufeto Janar Ibrahim Commassie, na shaida masa. Sai ya ce min, watau na fahimci cewa akwai iyakar abin da ba zai iya yin komai a kai ba.”

Obasanjo A Gaban Masu Bincike

Ba kamar yadda ‘Yar’Adua ya rika kasancewa a cikin damuwa ba, shi Obasanjo kar ya rika kallon kowa, ko gezau ba ya yi. Duk tambayar da aka yi masa, tamkar dama ya rigaya ya shirya amsoshin da zai bayar a cikin kwakwalwar sa.

“Akwai lokacin da aka shafe yini guda cur ana yi wa Obasanjo tambayoyi, amma ya rika bayar da amsa kai-tsaye.

” Mamaki kuwa sai lokacin da Obasanjo shi kuma ya juyo da na sa tambayoyin a kan wanda ya kulla masa sharrin, wato Bello Fadile. Obasanjo ya rika bayanai tiryan-tiryan da kawo ranaku da lokuta ba tare da ya na duba takarda ko daya ba.”

Farida ta kuma bada labarin yadda binciken sauran wadanda aka zarga ya kasance, kamar irin su Chris Anyawu, babbar ‘yar jarida, wadda daga baya har sanata ta zama da kuma irin yadda masu bincike suka rika gasa wa Lawan Gwadabe tsananin radadin azaba, har sai da ya kai ba ya iya mikewa tsaye!

Share.

game da Author