Bisa dukkan alamu Gwamna Obaseki na Jihar Edo ya samu yadda ya ke so, ganin yadda Jam’iyyar APC ta rusa Kwamitin Sasanta Rigingimun Jam’iyya a karkashin Shugaban Majalisar Dokoki, Ahmed Lawan.
A yanzu an cire Lawan daga shugabancin Kwamitin mai mutane 10 da aka nada tun cikin watan Disamba domin sasanta dukkan sabanin da ke tsakanin ‘yan jam’iyya a fadin kasar nan.
A yanzu an sake kafa wani Kwamitin mai mutane 12, amma a wannan karo, an zabi dattijo Bisi Akande ya zama shugaban kwamiti.
A wannan kwamiti da aka rusa dai Alande ne mataimakin shugaban kwamiti.
An rusa wancan kwamitin ne bayan Gwamna Obaseki na Edo ya ki amincewa da shugabancin Lawan, ya na mai cewa ai da hannun Lawan wajen kitsawa da ruruta rudanin siyasa tsakanin gwamnan da Shugaban APC na Kasa, Adams Oshiomhole.
Wancan lokaci Oshiomhole ya tsaya kan bakan sa cewa bai yarda da shugabancin sa ba, saboda, “Sanata Lawal da Kakakin Majalisar Tarayya, Abdullahi Wase su ne suka jagoranci zaman majalisar da aka zartas da rufe Majalisar Jihar Edo.
“Kuma su ne dai aka yi shari’a da su a babbar Kotun Tarayya ta Fatakwal inda kotun ta haramta wa Majalisar Tarayya ikon kwace Majalisar Dokokin Jihar Edo.
Sai dai har yanzu Wase na cikin kwamitin, kamar yadda Kakakin Labarai na APC, Lanre Issa-Onilu ya bayyana.
Onilu ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya sake nazarin kwamitin kuma ya canza shugabanci da wasu ‘yan kwamitin.
Sauran ‘yan kwamitin sun hada da Gwamnonin Neja da Osun, Sanata Yahaya Abdullahi, Tanko Almakura da Kashim Shettima da sauran su.
Ranar 11 Ga Fabrairu ne za a yi kwarya-kwaryar taron kaddamar da kwamitin a Hedikwatar Sakatariyar APC ta Kasa da ke Abuja.
Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga cikakken rahoton rigimar Obaseki da Oshiomhole makonni biyu da suka gaba.