Hukumar Bunkasa Ilmi a Manyan Makarantu, ta bayyana rashin jin dadin yadda malaman jami’o’i da na manyan makarantu da cibiyoyin ilmi ke karkatar da kudaden da ita TETFund din ke ba su domin su yi binciken da zai bunkasa ilmi.
TETFund ta ce ta gano yadda dimbin malamai ke karkatar da kudaden su na sayen motoci da saye ko Gina gidaje da wadannan kudade.
Wannan zargi ya fito ne kwanaki kadan bayan Hukumar ICPC ta bankado yadda wasu cibiyoyin ilmi da na kiwon lafiya suke yin aringizon makudan kudade a cikin kasafin kudaden su.
Mataimakin Daraktan Bincike na TETFund, Salisu Bakari ne ya yi wannan zargi ga malaman jami’a, a taron karin sanin makamar aiki da hukumar ke kan shurya wa waau malamai na jami’o’in Najeriya, a Dubai.
Ya ce su ma jami’o’in dungurugum ba a bar su baya ba wajen karkatar da kudaden bincike.
“Babbar cin amana ce a ba ka kudade domin ka gudanar binciken da zai inganta harkar ilmi ko wani fanni, amma ka karkatar da kudaden wajen data bushashar biyan bukatar ka.
“Mun yi binciken bin diddigi, sai muka bankado yadda malaman jami’o’i ke kwasar kudaden da TETFund ke ba su domin bincike su na sayen motoci da gina gidaje.
Daga nan sai Bakari ya yi dogon bayanin irin matakan da TETFund za ta dauka a kan wannan lamari.