PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Kotun Koli ta sabule wandon zababben gwamnan APC na Bayelsa, ta daura wa dan PDP.
Kotun Koli a ranar Alhamis ta tsige zababben gwamnan APC na Jihar Bayelsa, David Lyon, kwana daya rak kafin rantsar da shi.
Alkalai biyar da suka zauna domin yanke hukunci, a karkashin Mary Odili, sun ce sun soke nasarar zaben dan takarar APC ne saboda mataimakin sa Biobarakuma Degi-Eremienyo ya gabatar wa Hukumar Zabe (INEC) bayanan karya a kokarin sa na neman a wanke shi ya tsaya takarar mataimakin gwamna.
An yi zaben a ranar 16 Ga Nuwamba, 2019, tare da na jihar Kogi.
Kotun Koli ta amince ne da hukuncin da Babbar Kotun Bayelsa ta yanke tun da farko ta ce Biobarakuma bai cancanci tsayawa takarar mataimakin gwamna ba.
A hukuncin da Kotun Koli ta yanke, wanda Babban Mai Shari’a Ejembi Eko ya karanta a zaman kotun na karshe, ya umarci INEC ta kwace katin shaidar cin zaben da ta damka wa David Lyon da Dege-Eremienyo nan take.
Sannan kuma ya umarci INEC a damka katin shaidar cin zaben ga dan takarar da ya zo na biyu a zaben.
Wannan hukunci na nuna kenan dan takarar PDP, Diri Duoye ne za a rantsar a ranar Juma’a a matsayin gwamnan Bayelsa.
Duore ya zo na biyu da kuri’u 143,172. Shi kuma Lyon da aka tsige a ranar jajibirin rantsar da shi, ya samu kuri’u 353,552.
Shi kuwa Oshiomhole, kakkausan gargadi ya yi cewa kada a sake a rantsar da wani a ranar Juma’a idan dai ba David Lyon na APC ba ne.
Kotun Koli dai ta tabbatar da Douye ya samu adadin yawan kuri’un da INEC ke bukata kafin a tabbatar masa da nasarar zabe.
Kuma tun a ranar Alhamis hukumar zaben ta damka masa katin shaidar cin zaben gwamnan jihar Bayelsa, ta kwace wanda ta bai wa David Lyon na APC.
‘Oshiomhole Burin Kunya Ya Ke Yi’ – PDP
A martanin da ta maida masa, PDP ta ce borin kunya da surutan maras gaskiya ne kawai shugaban APC Adams Oshiomhole ke yi da ya ce kada a kuskura a rantsar da wani sai dan takarar APC.
Sai dai kuma Kakakin Yada Labarai na PDP, Kola Olagbondiyan, ya ce a yi kaffa-kaffa da Oshiomhole, domin kalaman sa na iya haifar da yamutsi a jihar Bayelsa.
“Su dai mutanen Bayelsa sun san INEC ba ta karbar umarni daga kowa a kasar nan, ballantana wani dan hauragiyar shugabancin bangaren wata jam’iyyar harmagaza mai suna APC.”
A karshe PDP ta roki al’ummar Bayelsa su kwantar da hankali, kada su bari wasu ‘yan jagaliya su tada hankulan al’ummar jihar.
Shi ma gwamnan jihar Rivers Wike ya gargadi Oshiomhole kada ya kuskura ya karat soma baki a batun rantsar da zababben gwamnan jihar Bayelsa, Diri Douye.

