Rundunar ‘Yan sandan jihar Bayalsa ta saka dokar hana zirga-zirga a jihar Bayalsa na kwana uku.
Hakan ya biyo bayan barkewa rikici ne a fadin jihar a daidai ana rantsar da Sabon gwamnan jihar Diri Duoye.
Rahotanni sun nuna cewa hasalallun matasa sun afka gidajen Sabon gwamna Diri na jam’iyyar PDP, da gwamna mai barin gado, Seriake Dickson inda suka Cinna musu wuta.
Idan ba a manta ba kotun koli ta warware nasarar da APC ta yi a zaben gwamnan jihar Bayalsa inda ta ce a dalilin sakamakon karya da dantakarar mataimakin gwamnan jihar ya Mika wa hukumar zabe.
A dalilin haka hukumar zabe ta soke duka kuri’un da APC ta samu a zaben ta nada Diri na PDP Sabon gwamnan jihar Bayelsa.
Kamar yadda APC ta yi murnar yin nasara a kotun koli a jihar Imo haka yanzu ‘Yan jam’iyyar PDP kemurnar nasarar jihar Bayelsa.
Cikin gidajen da aka har da wani sashen hedikwatar jam’iyyar PDP a jihar.
Discussion about this post