Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta tabbatar wa dan takarar PDP, Diri Douye nasarar lashe zaben gwamna a jihar Bayelsa.
Hakann ya biyo bayan soke zaben David Lyon na APC da Kotun Koli ta yi a ranar Alhamis.
Da ya ke jawabin kai-tsaye ga manema labarai, Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa “a bisa bin umarnin Kotun Koli, INEC ta nasar da cewa an cire APC daga cikin jam’iyyun da suka shiga takarar zaben gwamna a jihar Bayelsa, a ranar 16 Ga Nuwamba, 2019.
“A kan haka, mun bi umarnin kotu da ta ce a bai wa wanda ya zo na biyu nasara, wato dan takarar PDP, Douye Diri.
“INEC ta zauna ta yi nazari kuma ta tantance cewa dan takarar PDP ne ya fi sauran ‘yan takara samun kuri’u masu yawa a zaben Bayelsa.
“ Douye Diri ya samu kuri’u 143, 172. Shi kuma wanda ya zo na biyu, wato dan takarar jam’iyyar Accord Party, ya samu kuri’u 1,339. Bambancin kuri’u tsakanin PDP da Accord Party sun kai 141, 833.
“Saboda haka dan takarar PDP ya cancanci lashe zabe kamar yadda ka’ida ta tanadar. Yanzun nan ba da dadewa ba za mu damka masa safitiket din shaidar lashe zabe.”
Yakubu ya ce wa’adin gwamna mai ci a yanzu na Bayelsa zai kare a yau Juma’a, karfe 12 na dare.
Yadda Kotunn Kotun Koli Ta Sabule Wandon Lyon Ta Daura Wa Diri
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Kotun Koli ta sabule wandon zababben gwamnan APC na Bayelsa, ta daura wa dan PDP
Kotun Koli a ranar Alhamis ta tsige zababben gwamnan APC na Jihar Bayelsa, David Lyon, kwana daya rak kafin rantsar da shi.
Alkalai biyar da suka zauna domin yanke hukunci, a karkashin Mary Odili, sun ce sun soke nasarar zaben dan takarar APC ne saboda mataimakin sa Biobarakuma Degi-Eremienyo ya gabatar wa Hukumar Zabe (INEC) bayanan karya a kokarin sa na neman a wanke shi ya tsaya takarar mataimakin gwamna.
An yi zaben a ranar 16 Ga Nuwamba, 2019, tare da na jihar Kogi.
Kotun Koli ta amince ne da hukuncin da Babbar Kotun Bayelsa ta yanke tun da farko ta ce Biobarakuma bai cancanci tsayawa takarar mataimakin gwamna ba.
A hukuncin da Kotun Koli ta yanke, wanda Babban Mai Shari’a Ejembi Eko ya karanta a zaman kotun na karshe, ya umarci INEC ta kwace katin shaidar cin zaben da ta damka wa David Lyon da Dege-Eremienyo nan take.
Sannan kuma ya umarci INEC a damka katin shaidar cin zaben ga dan takarar da ya zo na biyu a zaben.
Wannan hukunci na nuna kenan dan takarar PDP, Diri Duoye ne za a rantsar a ranar Juma’a a matsayin gwamnan Bayelsa.
Duore ya zo na biyu da kuri’u 143,172. Shi kuma Lyon da aka tsige a ranar jajibirin rantsar da shi, ya samu kuri’u 353,552.
Shi kuwa Oshiomhole, kakkausan gargadi ya yi cewa kada a sake a rantsar da wani a ranar Juma’a idan dai ba David Lyon na APC ba ne.
Kotun Koli dai ta tabbatar da Douye ya samu adadin yawan kuri’un da INEC ke bukata kafin a tabbatar masa da nasarar zabe.
Kuma tun a ranar Alhamis hukumar zaben ta damka masa katin shaidar cin zaben gwamnan jihar Bayelsa, ta kwace wanda ta bai wa David Lyon na APC.
‘Oshiomhole Burin Kunya Ya Ke Yi’ – PDP
A martanin da ta maida masa, PDP ta ce borin kunya da surutan maras gaskiya ne kawai shugaban APC Adams Oshiomhole ke yi da ya ce kada a kuskura a rantsar da wani sai dan takarar APC.
Sai dai kuma Kakakin Yada Labarai na PDP, Kola Olagbondiyan, ya ce a yi kaffa-kaffa da Oshiomhole, domin kalaman sa na iya haifar da yamutsi a jihar Bayelsa.
“Su dai mutanen Bayelsa sun san INEC ba ta karbar umarni daga kowa a kasar nan, ballantana wani dan hauragiyar shugabancin bangaren wata jam’iyyar harmagaza mai suna APC.”
A karshe PDP ta roki al’ummar Bayelsa su kwantar da hankali, kada su bari wasu ‘yan jagaliya su tada hankulan al’ummar jihar.
Shi ma gwamnan jihar Rivers Wike ya gargadi Oshiomhole kada ya kuskura ya karat soma baki a batun rantsar da zababben gwamnan jihar Bayelsa, Diri Douye.
Discussion about this post