Gamayyar dakarun tsaron Najeriya dake aikin samar da tsaro a yankunan jihohin Zamfara, Kebbi da Katsina, sun yi nasarar dagargaza wasu gaggan ‘yan ta’adda 13 a harin da suka kai musu har maboyar su a dazukan dake kewaye da jihohin.
Dakarun sun yi nasaran dagargaza maboyan mahara sannan sun kashe akalla gaggan masu garkuwa da mutane 13.
Baya ga haka kuma sun kwato dubban harsasai da bindigogi, sannan sun cafke wasu da ke yi wa maharan jigilar muggan kwayoyi da makamai zuwa cikin kungurmin dazukan.
Garuruwan da aka kai wa maharan hari sun hada da Tungar Mata, Tuduki, Kawaye da Mararaban Kawaye duk dake karamar hukumar Anka, sannan kuma da garuruwan Moriki, Belhi, Ruwar Kura, Kyaram, Gallai da Shirkai duk a karamar hukumar Bukkuyum jihar Zamfara.
Sannan kuma da garuruwan Tsauwa, Dankar da Yan Gayya dake karamar hukumar Batsari, jihar Katsina, da Gallai, Shirkai da ‘Yarkuka duk a jihar Kebbi.
Dakarun Sojojin kasa, sama, ‘yan Sanda, Sibul Difens ne suka yi wannan aiki a tsakanin ranakun 10 zuwa 20 ga watan Fabrairu.
Discussion about this post