YOBE: Boko Haram sun fito da wani salon kisan matafiya

0

Boko Haram sun bude wa wasu ‘yan bijitanti wuta a kan hanyar Damaturu zuwa Gashua, kamar yadda wani jami’in ‘yan sa-kai ya shaida wa wakilin mu.

Jami’in, wanda ba ya so a ambaci sunan sa a jarida, ta ce tabbas an kashe ”yan bijilante da dama, kuma an kwace musu motar da da su ke sintiri a kan ta, samfurin Toyota Hilux.

An kai wannan mummunan hari, tsakanin kayukan Lantewa da Kaliyari. Boko Haram sun tare hanya, suka kafa shingen bincike kusan sa’o’i da yawa su na tare mutane.”

Kakakin Riko na ‘Operation Lafiya Dole 2, Chinonso Oteh, ya tabbatar da Boko Haram sun kai wannan hari, amma kuma ya ce an tura dakaru na kasa da kuma a jirgin yaki an ragargaji Boko Haram din.

Wani matafiyi da ya ce sunan sa Modu, ya ce ya sha da kyar yayin da ya dirka daga cikin mota, ya keta cikin daji ya yi ta tikar gudun-famfalaki.

“Sun rika tare motoci su na tambayar kowa ya nuna musu ID card din sa.

“Sun ce mana ba’arin mutane uku kawai suke nema, suke so su kama. Suka ce ana farko jami’in tsaro suke son su kama. Sai kuma ma’aikacin gwamnati, sai na uku kuma za su kama Kiristoci.”

Da aka zo kan sa, ya ce shi Dan kasuwa ne, dan tireda ne.

Ya ce a gaban su Boko Haram suka bi wata Hilux cike da jami’an bijilante. Motar ta kauce, ta fada wani kwari. Su kuma Boko Haram suka bude mata quta.

Ya ce irin yadda suka rika bude wa na cikin motar wuta, ya tabbatar ba su bar ko da mutum daya da rai a cikin motar ba.

Share.

game da Author