Hanan, ’yar Shugaba Muhammadu Buhari, ta bayyana cewa ita ba ta ma san jami’an tsaro na SSS sun kama wanda ya sayi layin MTN da ta taba amfani da shi ba.
Ta yi wannan ikirari ne biyo bayan maka ta kara kotu da wani mai suna Anthony Okolie ya yi, inda ya kai karar ta da kuma jami’an SSS, tare da yin zargin cewa ta sa SSS sun kulle shi tsawon makonni 10.
An kulle Okolie ne saboda samun sa da aka yi da layin waya na katin MTN, wanda Hanan ta taba amfani da shi a baya.
Lauyan Hanan mai suna M.E Sheriff ne ya cike fam a kotu cewa layin da aka samu mallakin Okolie, a da can baya Hanan ta taba amfani da shi.
Sai dai kuma ta ce ita ba ta da wata masaniyar cewa SSS sun kama wani mai amfani da lambar a yanzu.
A rubutaccen bayanin da lauyan hanan ya mika wa kotu, wanda PREMIUM TIMES ita ma ta mallake shi, ta bayyana cewa;
“Duk da dai a gaskiya ni ban ji dadin yadda jama’a ke ta korafin cewa akwai wani na amfani da wani layi na da na daina amfani da shi ba. Amma dai ni ban taba kai kuka ko korafi a hannun SSS ko wasu jami’an tsaro a nan Najeriya ko a wata kasa ba, ballantana har na ce wai su kamo wani.”
Hakan ta ce “an je kotu ana zargin ta da aikata abin da kwata-kwata ba ta ma san ya faru ba, kuma ba ta san komai a kai ba.”
Cikin makon jiya PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Okolie ya maka MTN, Hanan da kuma SSS Babbar Kotun Tarayya da ke Asaba, babban birnin jihar Delta, inda ya yi kukan an danne masa hakkin sa, an ci mutuncin sa, kuma ya nemi diyyar naira milyan 500.
Shi dai ya bayyana wa kotu cewa ya sayi layin a ofishin MTN, don haka bai ga dalilin da jami’an SSS za su kama shi su tsare, har makonni 10 ba, don ya sayi layin da ’yar shugaban kasa ta taba amfani da shi.
A ranar 12 Ga Fabrairu, Mai Shari’a Nnamdi Dimgba ya ragargaji lauyan Hanan, saboda ya shaida wa kotu cewa Hanan ba ta da ta cewa dangane da batun.