Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayyana cewa akalla mutane 24 ne suka rasu sanadiyyar kamuwa da zazzabin lassa a kasar nan.
Daga ranar 1 zuwa ranar 19 ga watan Janairu an yi wa mutane 398 daga jihohi 19 gwajin jini inda sakamakon gwajin ya nuna cewa mutane 163 na dauke da cutar sannan wasu 24 sun mutu.
Hukumar na hasashen cewa adadin yawan mutanen da suka kamu da cutar zai karu domin a cikin makonni Uku adadin yawan mutanen da suka kamu da cutar ya karu daga 64 zuwa 81 a jihohin Ondo, Edo, Delta, Filato, Taraba da Bauchi.
Hukumar ta kuma ce an gano cutar a jikin akalla mutum daya a kananan hukumomi 32 daga jihohi Tara.
Babu babba babu yara a mutanen dake kamuwa da cutar domin maza da mata masu shekaru 11 zuwa 40 na cikin wadanda suka kamu da cutar a kasar nan.
Idan ba a manta ba a ranar Talata ne PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda cutar ta bullo a jihar Ondo inda akalla mutane 16 suka rasu.
A ranar Laraba kuma mutane Uku sun rasu a jihar Kano sannan daya a jihar Enugu.
KIRA DOMIN AYI HATTARA:
1. Hukumar ta yi kira ga mutane cewa da zaran an kamu da zazzabi a nemi likita domin samun tabbacin abin dake damun mutum.
2. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbatar sun yi amfani da kayan aiki da gwajin da ya kamata a duk lokacin da zasu duba mai fama da zazzabi a asibiti.
3. Kamata ya yi ma’aikatan kiwon lafiya su ci gaba da yin taka tsan-tsan wajen kula da masu fama da cutar domin hana yada cutar.
YADDA ZA A GUJEWA KAMUWA DA ZAZZABIN LASSA
1. Tsaftace Muhalli: A rika tsaftace muhalli a ko da yaushe. A kau da datti a kowani lokaci sannan a rika goggoge wuarare.
2. Zubar da Shara: Idan aka tara datti, kada arika barin su kusa da gida. A kai su can wajen da ake zubdawa a nesa ko kuma a rika konawa.
3. Killace Abinci: Yin haka zai taimaka wajen hana bera ko kwari shiga cikin abincin.
4. Dafa Nama: Kafin a dafa nama kamata a rika wanke shi da ruwan gishiri domin kashe duk wasu kwayoyin cuta dake jikin naman. A tabbatar naman ya dahu sosai kafin a ci.
5. Namun Daji: A nesanta kai daga yin mu’amula da namun daji musamman jinsin berayaye da birai.
6. Cin ‘ya’yan itatuwa: Kafin a ci ‘ya’yan itatuwa ko kuma ganye a rika wanke su sosai. Hakan na kau da datti a jikin su.
7. A daina barin dabbobin gida na shiga inda ake aje abinci: Kaji da wasu dabbobin da ake kiwon su a gida kan yi mu’amula da beraye a lokutta da yawa.
8. Toshe kafafen da suka bude: A tabbatar an toshe ramin da bera zai iya shiga cikin dakunan mu.
9. Tsafta: A yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu kafin da bayan an ci abinci sannan idan an kammala amfani da ban daki.
10. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbata sun nemi magani da zarar allurar da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.
11. Kona Daji: Kona daji na daga cikin hanyoyin dake koro beraye zuwa cikin gidajen mutane. A rika kiyayewa wajen kona dazukan dake kewaye da mu. Mai makon haka a rika feshin magani.
12. Wanke gawa a cikin Daki: Shima hakan na da illa matuka. Maimakon a rika wanke gawa a cikin gida a rika yin sa a waje ne ko kuma inda ya kamata.