Fargaba da tararrabi na karuwa a fadin Jihar Barno, ganin yadda Boko Haram ke kai hare-hare kan babban titi daya da ya rage ake shiga jihar Barno.
Fargabar da jama’a ke yi shi ne yadda wannan yawan hare-hare ke naman datsewa ko raba jihar Barno da ga Najeriya.
Akwai manyan titina shida daga kusurwoyi daban-daban da ake shiga Maiduguri daga wasu sassan kasar nan.
Sai dai kuma shekaru shida kenan tun bayan da Boko Haram suka zage damtsen kai hare-haren ta’addanci, titina biyar duk ba su biyuwa, sai titi daya kawai ya rage a ke bi.
Wannan titi daya da ya rage kuwa shi ne mashigar Maiduguri daga Kano, Jigawa, Bauchi da Yobe.
Tsakanin 2013 zuwa 2014 dai Boko Haram duk sun karya gadojin da ke kan hanyar titina hudu na shiga Maiduguri, ta yadda babu yadda za a yi motoci su shiga Maiduguri daga wadannan hanyoyi. Sannan kuma sun mamaye wasu kauyuka da ke kan wadannan hanyoyi.
A yau daga Maiduguri zuwa Biu ya zama wata tafiyayya mai wahala. Tsakanin Biu da Maiduguri dai kilomita 180 ne.
BOKO HARAM: Da Sauran Rina A Kaba
Amma saboda hanyar ba ta biyuwa saboda tsoron Boko Haram, sai masu mota sun kewaya ta Yobe, Bauchi su zarce ta Gombe, wanda wannan kuwa tafiya ce tsawon kilomita 560.
Matafiya Gwoza daga Maiduguri dai tafiya ce ta kilomita 127 kawai. Amma a yanzu tilas sai sun kewaya ta jihar Adamawa, wadda tafiyayya ce ta daruruwan kilomita.
Al’amurran sun fi lalacewa a mazauna Arewacin Barno. Kafin Boko Haram su kwace titinan da suka doshi Gamboru har zuwa cikin kasar Chadi, da kuma titin Mobbar zuwa Gubio har cikin Najar, matafiya musamman masu cinikin kifi da fatu, sukan yi wannan doguwar tafiyar fatauci tsakanin Najeriya, Chadi da Nijar.
Cikin Disamba, 2018, sojoji sun bude wadannan hanyoyi bayan sun yi ikirarin cewa “sun kwato” titinan daga hannun Boko Haram.
Sai dai kuma hanyar ba ta biyuwa sai da rakiyar jerin kwamba din sojoji masu yi wa dandazon daruruwan motocin matafiya rakiya.
Duk kuma da wannan shirin yaki da sojoji kan yi idan za su raka motocin, hakan bai hana Boko Haram yi musu kwanton-bauna su na bude musu wuta ba.
To a yau dai wadannan hanyoyi da sojoji suka ce sun bude, duk wanda ya bi su, to sai dai daga can ya zarce lahira kawai.
Kowa da kowa, kowa da komai, komai da komai ba mai iya shiga Maiduguri a yau sai ta wannan hanya daya kwal, watau hanyar shiga Maiduguri daga Damaturu, wadda ta taso daga Fataskum daga da Dutse. Ita ce dai ta taso tun daga Kano.
Matafiya daga Jos, Kudu maso Gabas, Bauchi, Adamawa da Gombe da Taraba kuwa, daga Fataskum su ke hawan wannan hanya su doshi Maiduguri.
To kuma wannan babbar hanya daya da ta rage ce Boko Haram a yanzu ke ta kai wa hare-hare kusan tsawo wata daya kenan ana kai wa juna juna dauki a kan hanayar tsakanin sojoji da Boko Haram.
Dakarun Tsaron Titin Shiga Maiduguri Daga Kano
Dakarun da ke gadin titi daya tal da ya rage shiga Maiduguri daga Kano da sauran dukkan jihohin Najeriya, sun hada da Sojoji, SARS sai kuma CJTF.
A baya an dade ba a kai wa titin hari ba, tun bayan wanda Boko Haram suka kai a Benisheik, hedikwatar Karamar Hukumar Kaga cikin Jihar Barno.
Benishiek babban gari ne kan hanyar shiga Maiduguri daga Damaturu.
Katsam, yayin da Boko Haram suka waiwayo kan wannan babban titi a cikin 2019, sun dira garuruwan Mainok, Jakana, Ngamdu da Kukareta.
Mainok, gari mai nisan kilomita 10 kacal daga Benisheik, sai da Boko Haram suka kusa tarwatsa shi, amma ba su mamaye shi ba.
Gadar Benishek, Gadar Shiga Maiduguri
Akwai gada a Benishek, wadda ita kadai ce gada daya tilo daga Damaturu har zuwa Maiduguri, tafiyar kilomita 135.
Wannan gada dare da rana, safe da yamma, awa 24 sojoji na gadin ta. Saboda Boko Haram sun yi ta kokarin karya gadar, amma ba su yi nasara ba.
Tun daga 2012 har yau din nan, ita kadai ce babban dalilin da ya sa ake iya shiga jihar Barno ko ma daga ina, in dai ba a jirgin sama ba.
Matsawar Boko Haram suka karya wannan gada, to sun datse Maiduguri ko ma a ce Jihar Barno daga Najeriya.
Boko Haram Ba Su Hakura Ba
Tun bayan artabun Gwamna Babagana Zulum da sojoji a kan hanyar, inda ya nuna rashin jin dadin yadda suke karbar kudi ga matafiyan da ba su da katin shaidar dan kasa, Boko Haram ba su daina kai hare-hare a kan titi daya tal da ya rage shiga Maiduguri ba.
Ranar 9 Ga Janairu, sun kai hari a Auno, kilomita 23 gada Maiduguri. Suka tare motar fasinja, suka ji awon-gaba da matafiya bakwai.
Washegari ne Gwamna Zulum ya bai wa jami’an tsaro motoci Hilux sabbi garau domin sintirin tabbatar da tsaro a jihar.
Duk wannan bai hana Boko Haram ci gaba da kai hare-haren tare hanyar shiga garin Maiduguri ba akai-akai.
Ranar 13 da 16 Ga Janairu dai sun sake tare matafiya inda suka kwashi matafiya da yawa, ciki har da wani dan asalin Jihar Filato, dalibin Jami’ar Maiduguri, wanda a ranar Litinin din nan suka saki bidiyon yadda suka yi masa kisan gilla.
Wani dalibin da suka arce da shi, sun sake shi bayan ya kantara musu karya, ya bayyana musu cewa shi kwas din Larabci ya ke nazari.
Ya ce bayan sun gudu da shi, sai da suka sake dawowa da shi har Auno, inda suka tare hanya suka yi awon-gaba da shi.
Yayin da gwamnatin tarayya, ta jihar Barno da Yobe da Rundunar Sojojin Najeriya ke ta kokarin nuna irin ci gaban da ake samu wajen yaki da ‘yan ta’adda, shi dai talaka babu ruwan sa da bambanci tsakanin ISWAP da Boko Haram.
Makashin ka makashin ka ne, ko da soshiya ya kashe ka, ba ma bindiga da bama-bamai ba.