Yadda za a rika tafiyar da ayyukan Dakarun Amotekun – Shugaban Kirkiro Dakarun

0

A wata tattaunawa ta musamman da ya yi da PREMIUM TIMES, Shugaban Hukumar Musamman Domin Inganta Shiyyar Kudu Maso Yamma (DAWN), Adetayo Adeleke-Adedoyin, ya tattauna yadda za a tafiyar da dakarun.

Ya bayyana cewa tun bayan kaddamar da dakarun a ranar 9 Ga Janairu, su na ta kokarin ganin an fara komai ya kankama, daga nan kuma sai a fara sakin dakarun da kuma tulin motocin da aka tanadar musu domin fara aikin tsaro.

Ya ce duk da surutan da ake ta yi, babu wani abu da ya tsaya dangane da tafiyar da Amotekun. Ya ce sun a nan su na gudanarwa, kuma har yau ba su samu wani sako ko umarni ko sanarwar cewa su tsaya ko su fasa ko su saurara ba.

Da aka tambaye shi batun daukar ma’aikatan tsaron, sai ya ce jihohi ne ke aikin daukar ma’aikatan, ba wai hukumar sa ta DAWN ba.

“Mu a DAWN abin da kawai muka yi, shi ne bai wa kowace jiha irin ka’ida da sharudda da yanayin irin wadanda za a dauka wannan aiki na Amotekun. Kuma sai matashi ya cika wadannan sharudda sannan za a iya daukar sa wannan aiki.

Da aka tambaye shi wadanne hanyoyi ne za a rika tafiyar da Amotekun, musamman batun kudaden tafiyarwa, gudanarwa da batun biyan albashi da sauran dawainiyar yau da kullum.

Sai Adedoyin ya bayyana cewa duk wadannan jihohi kamar Ogun, Ekiti, Oyo da Lagos duk su na da Gidauniyar Kudaden Tsaro da aka dade ana tarawa wasu ma tun kamar shekaru uku da suka gabata kenan ake tara kudaden.

“Sannan kuma abin lura dai shi ne, kowace jiha ita za ta rika tafiyar da dawainiya da nauyin Dakarun Amotekun na jihar ta.

“Ya rage ga kowace jiha ta san abin da za ta rika biya na albashi. Kuma zai iya yiwuwa wata jihar ta fi wata biyan albashi mai dan kwari.

Akwai kuma Dakarun Iromole da za a dauka, na wucin-gadi a karkashin Amotekun. Wadannan su a kan babura za su rika shiga lunguna da sakon da mota ba ta iya shiga.

Akwai jama’a da dama mazauna yankin Kudu maso Yamma da ke tsoron za a yi amfani da wadannan dakaru a kan su. Sannan kuma akwai masu adawa da ke gudun cewa gwamnoni za su iya amfani da Amotekun su rika yi musu dirar mikiya.

Amma a kan haka, Adedoyin ya ce tun da garkuwa da mutane da kisan mutane ana tsafi da su ya yi tsamari, ba a kai wa wani ko wasu rukunin jama’a hari don ana zargin su ba.

Sai ya ce tunda har ba a yi hakan ba, to a yanzu ma ba za a yi amfani da Amotekun a kan masu adawa ko wadanda ba a’yan asalin jiha ba.

Dangane da wadanda ke zargin gwamnoni sun kafa ‘yan barandan su don yi musu banga da jagaliyancin siyasa kawai, ya ce wannan tunani ne na su, amma kowa ya san hakan ba mai yiwuwa ba ne. Kuma ba don haka aka kafa rundunar ba.

Share.

game da Author