ZAMFARA: Mahara sun sace mutane biyar a Karamar Hukumar Bukkuyum

0

Mahara har 20 sun arce da mutane biyar daga kauyen Dogon Daji Sarkin Noma, dake karamar hukumar Bukkuyum.

Kamar yadda wani mazaunin kauyen Dogon Daji ya bayyana, ya ce maharan sun kai 20 da suka farwa kauyen.

” Bayan kwakkwace abubuwan da suke so sai suka ba mu lambobin waya da za mu nemi akai sannan suka tafi da mutane biyar. Maza hudu mace daya.”

Wadanda aka arce da su sune Hakimi Danjuma, Anas Isa, Buba Hakim, Lawalli Olu da Yahanasu Jamilu.

Harin Gumi

Wani mazaunin kauyen Babban Rafi da ke karamar hukumar Gumi, jihar Zamfara ya bayyana yadda mahara suka afka wa kauyen suka kashe mutane da dama.

Wannan mazauni da baya so a fadi sunan sa ya bayyana wa manema labarai cewa maharan sun shigo Babban Rafi ne a kan babura su akalla sama da 30 sannan suka barin wuta da bindigogi ta ko ina.

“ Mun samu labarin cewa kafin maharan su afka mana sun kai hari kauyen Barikin da Daji inda anan sai da suka sace dabbobi da duk wani abu da suka gani suna so.

” Mun yi jana’izar mutane akalla 20 da maharan suka kashe. Sannan kuma akwai da dama da suka bace da har ya zu ba mu san inda suke ba.

Idan ba a manta ba a cikin makon da ya gabata ne wasu mahara suka far wa kauyen Makosa dake karamar hukumar Zurmi inda suka kashe wasu ma’aikatan kiwon lafiya biyu nan take.

Maharan sun kashe wadannan ma’aikata ne a lokacin da suke yi wa yara allurar rigakafi a cibiyar kiwon lafiyar dake kauyen.

Share.

game da Author