Na kashe budurwa ta Nafeesat saboda gudun barin abin kunya – Mustapha

0

Wani matashi mai suna Mustapha Idris, mazaunin karamar hukumar Ringim, jihar Jigawa ya shaida wa wakilin mu cewa ya kashe budurwarsa Nafeesat Hashim ne a saboda gujewa barin abin kunya a garin su.

Mustapha da Nafeesat dai saurayi ne da budurwa sai dai a zamantakewar su sun yi kusanta matuka da ya kai ga Mustapha ya dirka wa Nafeesat ciki.

Bayan cikin ya kai wata uku sai Mustapaha ya yanke shawarar kawai bari ya kashe ta gudun kada ta haihu ta jawo masa abin kunya a garin su.

Da yake suna zama a kusan gida daya ne sai Mustapha ya tafi bayan gari da Nafeesat inda a nan ne ya kashe ta.

Kakakin rundunar ‘Yan sandan jihar Jigawa Audu Jinjiri ya bayyana cewa Mustapha ya amsa laifin sa.

Ko da muka gudanar da bincike mun gano cewa Mustapha ne ya kashe Nafeesat.

” Mustapha ya ce gudun ya bar abin kunya ne ya sa ya kashe Nafeesat kawai da dan dake cikin ta yadda gobe ba za ace ga dan sa da ya haifa da Nafeesat ba a aure ba.

Jinjiri ya kara da cewa sun iske Nafeesat kwance male-male cikin jini a inda ya jefar da gangan jikin ta.

Nafeesat bazawara ce, ta taba aure.

Share.

game da Author