TA KACAME: Oshiomhole bai isa ya hana ni sake tsayawa takarar gwamna ba -Gwamna Obaseki

0

Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa Adams Oshiomhole bai isa ya taka masa burkin sake tsayawa takarar zaben Gwamnan Jihar Edo ba.

Obaseki, wanda shi ne ya gaji Oshiomhole bayan kammala zangon sa ba biyu na gwamnan Edo, ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya ke ganawa da shugabannin APC na Karamar Hukumar Eredo, a shirin kamfen din zaben gwamna da za a yi a Edo cikin 2020.

An dai samu mummunan sabanin siyasa tsakanin Obaseki da Oshiomhole, wanda har yau an kasa sasanta su.

Ana zargin Oshiomhole na goyon bayan wani dan takarar gwamna mai suna Osagie Eze-Iyamu, ba Obaseki ba.

Cikin wata sanarwar da kakakin yada labarai na Gwamna Obaseki, mai suna Crusoe Osagie ya aiko wa PREMIUM TIMES, ya ce, “hankalin gwamna na wajen zaben gwamna, ba kan takarar zaben fidda-gwani ba. Za a yi zabe kuma shi ne za a cimma yarjejeniyar tsaidawa.”

Obaseki ya ce ya dauki alkawari tun farkon shigar sa siyasa cewa zai kawo karshen siyasar ubangida a jihar Edo, kuma zai yi nasara.

Ya ce Oshiomhole ya yi kadan ya maida kan sa tamkar wani ubangiji a Edo, wanda wannan lalata siyasa ce ba inganta ta ba.

“Oshimhole da kan sa ya same ni ya ce na zo mu hada karfi mu kori siyasar ubangida a Edo. A haka Na goya masa baya ya yi shekaru takwas. Amma wai kuma shi ne a yanzu zai ce siyasar ubangida na da kyau.

“Duk aiyasar da babu kishin jama’a sai son kan ubangida, to wannan ba abin arziki ba ce.” Inji Obaseki.

Share.

game da Author