Gwamnan Jihar Ekiti ya bayyana cewa nan da ranar 9 Ga Janairu, 2020 ne Rundunar Tsaron Jihohin Kudu Masu Yamma za ta fara aiki gadan-gadan don kara infanta tsaron jihohin.
Rundunar mai suna ‘Western Nigeria Security Network’, jihohin Yamma da suka had a da Ekiti, Oyo, Ondo, Ogun Lagos da Osun ne suka kirkiro su.
Fayemi ya yi bayani a lokacin jawabin sa na sabuwar shekara ga al’ummar Jihar Ekiti cewa matsalar tabarbarewar tsaro ce ta sa tilas jihohin suka kirkiro wadannan jami’an tsaro, domin su taimaka wa sauran jami’an tsaro na gwamnatin tarayya wajen kara samar da tsaro.
Ya yi kiran da a ba sabbin jami’an tsaron goyon baya dari bisa dari domin su yi wa jama’a aiki.
Sannan kuma ya ja hankalin jama’a su guji yada labarai na karya a soshiyal midiya. Ya ce sahihan bayanin inda ake da matsalar tsaro wadannan sabbin jami’ai ke bukata, ba labarai marasa tushe, inganci da malama ba.
An dai dade ana dawurwurar samar da dokar da za ta bai wa kowace jiha damar kafa na ta ‘yan sanda, ganin yadda tun a shekarun baya tsaro dai kara tabarbarewa ya ke yi, kuma ana ganin ‘yan sandam kasar nan sun yi kadan matuka.
Sai dai kuma mafi yawan masu adawa da hakan na kafa dalili ne cewa, gwamnonin jihohi za su rika amfani da ‘yan sandan jiha su na musguna wa bangarenl masu adawa.