Kamar yadda kafar yada labarai ta Bloomberg, wadda ke da inganci da sahihanci ta fitar da rahoto, hamshakin dan kasuwa Aliko Dangote ya samu karin arziki cikin shekarar 2019 har na dala bilyan 4.3.
Hakan na nufin a yanzu arzikin Dangote ya haura dala bilyan 15 kenan, wannan ne kuma ya kai shi a matsayin na 96 a jerin masu arziki na dumiya a halin yanzu.
Dangote wanda shi ne ya fi kowa makudan kudade a Afrika, kuma bakar fatan da ya fi kowa kudi a duniya, ya samu karin makudan kudade ne cikin 2019 ta dalilin kasuwancin siminti, filawa da sukari.
Ya fara kasuwanci ya na da shekaru 21 a duniya. Ya kafa masana’antu masu da dama a Najeriya da wasu kasashe na Afrika.
A halin yanzu ya na gina katagariyar matatar mai da ake ganin ta na daga cikin mafi girma a duniya.
Tuni an fara jibge lodin kayan aiki a Lekki, cikin Lagos inda aikin ginin matatar ya kankama.
Ya fi kowa harkar kasuwancin siminti a Afrika, inda ya ke da masana’antu da dama a kasashe daban-daban na Afrika.
Idan za a kwatanta dala bilyan 15 da Dangote ya mallaka da naira, to sai a lissafa kowane dala bilyan daya na daidai da naira bilyan 360 kenan.