A shekarar 2019 jarumai da dama sun burge, wasu kuma sun nuna jarumtakar su wajen isar da gudunmawarsu don ci gaban al’umma, wasu kuma sun samu karramawa ne ba a cikin Najeriya ba kawai har daga kasashen waje
PREMIUM TIMES HAUSA ta tsamo wasu jarumai da suka samu ire-iren wadannan karramawa da isar da gaba ga al’umma.
1 – Zango ya biya wa yara marasa galihu 101 kudin makaranta na shekara uku da ya kai naira miliyan 47
Zango ya biya wa yara marasa galihu 101 kudin makaranta na shekara uku da ya kai naira miliyan 47 a wata makaranta dake Zariya.
Hukumar makarantar ta tabbatar da haka ta kuma jinjina wa jarumi Zango bisa wannan hubbasa da yayi na taimakawa yaran da iyayen su ba su da karfin iya biyan kudin makarantar ‘ya’yan su.
2 – An karrama Fati Washa da Rahama Sadau a Landan
A cikin shekarar 2019, wasu dava cikin fitattun Jaruman Kannywood suka samu karramawa a kasar Birtaniya.
An karrama Fati Washa a bukin karrama jaruman jaruman kasashen Afrika na 23 da aka yi a garin Landan.
Fati Washa ta lashe kyautar jarumar da tafi kowa shanawa a farfajiyar fina-finan Hausa a 2019.
Ta yi nasara a bisa jarumtar ta a fim din Sadauki. Ta doke abokanan aikin ta Aisha Tsamiya da Halima Ateteh.
Bayan haka an karrama Rahama Sadau da kyautar fitacciyar yar wasa a shekarar 2019. Shima jarumi Ali Nuhu ya samu wannan kyauta.
3 – An nada Fati Nijar Sarauniyar Mawakan Hausa dake Nahiyar Turai
Fitacciyar mawakiyar Hausa kuma ‘yar wasar fina-finan Kannywood ta sha ruwan yabo da jinjina daga dubban masoyan ta a dalilin karramawa da ta samu a kasar Faransa.
An karrama Fati a da sarautar Gimbiyar Mawakan Hausa dake nahiyar Turai.
Wannan kasaitaccen biki dai ya auku ne a fadar sarkin Hausawan kasashen Nahiyar Turai Alh Sirajo Jan Kado a garin Paris kasar Faransa.
Baya ga Fati Najeriya, an nada wasu mata biyu Jakadiyar Sarki da Giwar Mata.
4 – An karrama Ali Nuhu a Indiya
Fitaccen dan wasan fina-finan Hausa Jarumi Ali Nuhu ya samu karrama daga daliban Najeriya dake Kasar Indiya.
Daliban sun gayyace jarumi Ali ne domin bikin ranar ala’adu ada ake yi a kasar duk shekara ranar Juma’a 18 ga watan Oktoba.
A wajen bukin an saka wa Jarumi Ali Nuhu kayan kwalliya irin na mutanen indiya sannan kuma har an kalli wasu daga cikin fina-finan da jarumin yayi na Kannywood.
Ali Nuhu ya tattauna da jaridar BBC Hausa inda ya ya bayyana jin dadin sa game da wannan karramawa da daliban Najeriya dake kasar Indiya su ka yi masa.
” Daliban na karanta fanni daban-daban kama daga fannin likita zuwa hada magunguna da injiniya da dai sauransu. Sannan wasu daga cikin malaman har fina-finan Hausa suke kallo saboda su ga yadda yanayin rayuwar Bahaushe ta ke.” Inji Ali Nuhu.
5 – Maryam Booth ta zama wakiliyar talla na kamfanoni wayar sadarwa ta Airtel da Kamfanin Sinadarin Dandano na Ajinomoto.
Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa da ta shahara wajen kwalliya da gyaran jiki, sannan ta kware wajen fasahar iya rangwada da jarumta a harkar fina-finan Maryam Booth ta rattaba hannu a takardar yarjejeniyar zama wakiliyar talla na kamfanonin Airtel da Ajinomoto.
A hira da tayi da wakilin PREMIUM TIMES, Maryam ta tabbatar mana da haka inda ta kara da cewa a wannan shekara zata cigaba da burgewa domin lulawa da samun zama wakiliya a wasu manyan kamfanoni.
Discussion about this post