RUSA GIDAN SARAKI: Gwamna AbdulRazaq ya wuce gona da iri – Inji Gbemi Saraki

0

Karamar ministar Sufuri Gbemisola Saraki ta bayyana cewa lallai a wannan karo gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya wuce gona da iri rusa gidan mahaifin su marigayi Olusola Saraki da yayi.

Gbemisola ta ce bayan rusa gidan da yayi ya umarci jami’an tsaro a jihar da su jejjefa wa tsoffin mata da ke zanga-zangar rusa gini barkonun tsohuwa sannan wai sun rika harbin tsoffin da bindiga.

Sanarwan da kakakin ministan ta saka wa hannu ta kara da cewa lallai gwamna AbdulRazaq bai yi zurfin tunani ba kafin ya aikata wannan abu.

Idan ba a manta ba wan minista Gbemi, kuma tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, ya gargadi gwamnan da kada ya kuskura ya rusa ginin amma kuma cikin dare ya aika a ka rusa ginin.

Saraki ya yi ikirarin cewa sai fa inda karfin sa ya kare kan wannan abu da gwamnan jihar yayi.

Ya ce zai kai karar gwamnati kotu domin abi wa iyalan marigayi Olusola Saraki hakkin su.

Ya kara da cewa ba gaskiya ba ne cewa da gwamnati tayi wai da karfin tsiya marigati saraki ya mallaki wannan fili, in da ya gina wannan gida.

” Mahaifin mu ya mallaki wannan fili ne tun a 1980, kuma akwai takardun a kasa. Wannan abu da gwamna AbdulRazaq yayi siyasa ce kawai. Dama can akwai dadaddiyar kiyayya a tsakanin sa da iyalan Saraki. In ba haka ba me ya sa zai rusa wannan tsohon gina haka kawai.

Share.

game da Author