SSS sun damke wanda ya fara watsa bidiyon rudanin ‘ruguntsumin’ auren Buhari

0

Jami’an SSS sun bada sanarwar cewa sun damke mutumin da ya fara hada bidiyo sannan ya watsa mai dauke da rudanin ruguntsumin auren bogin Shugaba Muhammadu Buhari da Ministar Harkokin Kudade da Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed.

Wannan bidiyon bogi dai ya kuma nuna rududun auren shugaban kasa da Ministar Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Al’umma, Sadiya Umar-Farouq.

Wanda ake zargin da an gabatar da shi a hedikwatar SSS da ke Abuja, mai suna Kabiru Mohammed, mai shekaru 32 da haihuwa, kuma mutumin Kano ne.

Kabiru ya na da satifiket na difloma a Hausa, Fulfulde daga Babban Kwalejin Ilmi Mai Zurfi ta Tarayya, FCE Kano.

Sannan kuma ya na da difiloma a aikin sadarwa, ko kuma a takaice aikin jarida daga Kwalejin Addinin Musulunci ta Kano.

Kakakin SSS, Peter Afunanya, ya bayyana cewa wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa shi dan Kwankwasiyya ne, kuma ya amsa da bakin sa cewa shi ne ya hada bidiyon, sannan ya fara watsa shi.

Afunanya ya ce sun fara binciken salsalar bidoyon bayan da Ministar Harkkokin Kudi ta shigar da korafi da kan ta.

“Zainab Ahmed ta shigar da korafin ranar 11 Ga Oktoba, 2019, bayan da aka watsa bidoyon cikin watan Agusta da Satumba.

Ta ce wannan bidiyo ya kunyata ta, sai ta shigar da korafin a gano salsalar inda bidiyon ya fara fitowa.”

Ya ce ana ci gaba da binciken salsalar wannan batu domin gano makasudin yadda aka kitsa zancen.

Share.

game da Author