Hukuncin kisa ta hanyar rataya da kotuta yanke wa Maryam Sanda wacce kotu ta kamata da laifin kashe mijin ta Bilyaminu Bello a 2017 aya ce ga mata masu irin wannan hali, har ga maza masu irin halin.
Da za a rika kashe duk wanda ya kashe wani da gangar kamar yadda Allah ya ce, da an samu saukin yawan kisan kai a kasar nan. Domin duk wanda ya tabbata idan ya/ta kashe wani za a kashe shi/ta, toh ba wanda ya ke son mutuwa, saboda haka za a kiyaye ko ba don Allah ba, ko don aci gaba da rayuwa.
Amma idan za a rika kyale mutanen da suka yi kisa da gangar, kotu su yi ta jan kafa akan shari’arsu, daga karshe a kyale su, to, wannan ya sabawa hukunci Allah, kuma za a rika samun yawaita kisa saboda mutum ko yasa ko ya yi kisa ba abinda za a yi mishi bane. Amma ya manta akwai abinda Allah zai yi mishi idan ya mutu, domin dole shima sai ya mutu.
Na sani cewa Maryam Sanda ko da gangar ta kashe mijin ta, ko bisa kuskure ne, nasan tana cikin mai yin nadama sosai a yanzu.
Saboda haka ya kamata mu yi kokarin fin karfin zukatan mu duk lokacin da ran mu ya baci, kuma muka tsinci kan mu cikin wace matsala tare da rokon Allah ya kara bamu ikon fin karfin zukatan mu.
Ina mai matukar tausaya wa Maryam Sanda na halin da ta shiga, haka na suma iyaye da ‘yan uwan marigayi Bilyaminu Bello na irin halin harishin shi da suka yi ta fama da tun a lokacin da suka rasa shi zuwa yanzu. Allah ya kyautata karshen mu Amin
Allah ya ba mu zaman lafiya a kasarmu Najeriya.