An Bada Belin Shehu Sani

0

Mai Shari’a Inyang Ekwo ya bada belin Shehu Sani a kan kudi naira milyan 10. Sannan kuma ya ce wanda zai tsaya belin ya kasance ya na da wani fili ko gida na sa na kan sa.

Sharadi na gaba kuma shi ne Shehu Sani zai mika fasfo din sa ga rajistara na kotun, wanda kuma shi ne dama zai tantance sanihanci da cancantar mai beli.

An kuma haramta wa Sani fita kasar waje ba tare da sanar da rajistara na kotun ba.

EFCC ta gurfanar da Shehu Sani a kotu

Hukumar EFCC ta gufanar da tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani a kotu.

An tsare Shehu Sani tun cikin watan Disamba, 2019, a kan zargin ya karbi dala 25,000 a madadin Shugaban Hukumar EFCC, Ibarahim Magu, domin nema wa Alhaji Sani Dauda alfarma.

Sani Dauda shi ne mai kamfanin saida motoci na Kaduna, ASD Motors.

A kotu dai Sani ya ce bai aikata laifin ba, kamar yadda aka karanto zargin da ake yi masa.

An gurfanar da Sani a Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, a gaban Mai Shari’a Inyang Ekwo.

Cajin da ake yi wa Shehu Sanin a farko shi ne ya karbi dala 15,000 daga hannun Sani Dauda domin ya bai wa Cif Jojin Najeriya, Tanko Muhammad, domin ya samu sauki kan wata matsalar sa da ke kotu.

Sai kuma zargi na biyu, shi ne na karbar dala milyan 10 daga hannun Sani Dauda, domin ya bai wa Magu, shugaban EFCC.

Idan ba a manta ba, a bayan kama Shehu Sani, ya fito da sanarwa har sau biyu cewa duk karairayi ne da sharri ake kulla masa. Kuma kamar yadda ya ce, ba za su yi tasiri a kan sa ba.

Bayan an karanto masa laifukan da ake tuhumar sa da aikatawa, lauyan sa A A Ibrahim ya nemi a bada beli.

Sai dai kuma lauyan EFCC, Abba Mohammed ya roki kotu ta tsare Sani a kurkuku.

Daga nan sai Mai Shari’a ya ce a ba shi wani dan takaitaccen lokaci domin ya yi nazarin yanayin yadda karar ta ke zuwa wasu sa’o’i kadan. bayan haka sai ya bada da belin Sanatan.

Share.

game da Author