Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta yi tir tare da rashin jin dadin yadda ‘yan bangar siyasa suka yi rashin mutunci a zabukan da aka gudanar ranar Asabar a Jihar Akwai Ibom.
An gudanar da zabukan da ba su kammalu ba ne a Essien, inda nan ne mazabar da aka sake zaben sanata, tsakanin Chris Ekpenyong na PDP da kuma Minista Godswill Akpabio na APC.
Chris ya samu kuri’u 147, 714 shi kuwa Akpabio ya samu 83,820. A zaben Dan Majalisar Tarayya na mazabar ma PDP ce ta yi nasara, inda dan takarar ta ya samu kuri’u 17,990, shi kuma na APC ya samu 8,718.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda ‘yan bangar siyasa suka yi garkuwa da jami’an zabe zuwa wani lokaci a cikin sakandare.
Yayin da aka zargi Ministan Harkokin Neja Delta, Akpabiyo da daukar nauyin wadanda suka hargitsa zaben a a mazabar ta Akpabio.
Ministan dai ya musanta wannan zargi ta bakin kakakin yada labaran sa.
INEC ta ce abin takaici ne ganin yadda wasu ‘yan siyasa ke son maida Najeriya da tsarin dimokradiyya da na zabe baya, tq hanyar daure wa ‘yan sara-suka gindi su na hargitsa zabe.
Hukumar ta ce duk da irin yadda ta’asar da wannan bai hana a kammala zaben har a bayyana wanda ya yi nasara ba.
Idan za a tuna bayan Akpabio ya fadi zabe, ya kai kara kotu. Sai dai kuma bayan an ba shi mukamin MInista, sai ya ce ya fasa shiga sauran zaben da za a sake, wanda INEC ta ce ya janye a makare.
Discussion about this post