Fadar Shugaban Kasa ta bayyana mutuwar Shugaban Hukumar Makamashin Atom, tare da dan sa da kuma wasu mutane biyar yayin fashewar tukunyar gas a Kaduna.
Fadar ta ce akalla mutane biyar suka mutu a lokacin da gas din ya yi bindiga, tare da raunata wasu da dama.
Daga nan Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna jimami da bakin ciki da lahinin rashin shugaban hukumar, na ‘Nigeria Atomic Energy Commission, Simon Mallam tare da dan sa da kuma wasu mutane uku, a fashewar tukunyar gas din da ta faru a Sabon Tasha, jihar Kaduna, ranar Asabar da ta gabata.
Dama tuni PREMIUM TIMES ta buga labarin fashewar tukunyar gas din da ta faru ranar Asabar da rana.
Baya ga mutane biyar da Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa sun rasa rayukan su, an kuma kiyasta cewa dukiya ta milyoyin nairori ta kone kurmus a wurin da kewayen sa.
Mazauna unguwar sun ce tukunyar gas din ta yi bindiga a wani wurin da ake dura gas, inda wutar da tashi ta ritsa da mutane da yawa da ke kewayen wurin.
Shaguna da dama, mafi yawa na masu aski da gyaran gashi da masu kayan gini da kayan suturun zamani da sauran su duk sun yi asarar kayayyakin su.
Har yau dai ba a san sanadiyyar tashin gobarar ba, amma gwamnatin Jihar Kaduna ta ce za ta bincika ta gano musabbabin.
Da ya ke bayani da ta’aziyya, Shugaba Buhari ya ce, “Hankali na ya tashi sosai, kuma zuciya ta, ta yi baki matuka, jin wannan mummunan al’amari da ya kashe Farfesa Simon Mallam, tare da dan sa da kuma wasu da abin ya ritsa da su.
“Mutuwar Farfesa Mallam, asara ce da Najeriya ta yi na mashahurin farfesa ilmin kimiyya, wanda ya bar duniya a daidai lokacin da kasar nan ta fi matukar bukatar gudummawar sa a fannin kimiyya da fasaha, domin inganta kasar.’’
Ga sunayen wadanda aka tabbatar sun rasu a wannan hadari.
(1) Prof. Mallam Simon M
(2) Wale Ajayi M
(3) Daniel Peter M
(4) Victor Asoegwu M
(5) Micheal Ernest M