Rundunar ’Yan Sanda ta Kasa ta bayyana umarnin bayar da shirin ko-ta-kwana ga dukkan ‘yan sandan kasa baki daya, a fadin kasar nan.
Wannan ya biyo bayan abubuwan da ake fargabar tunzirin da su ke ganin ka iya faruwa a kasar nan, tun bayan kisan Babban Kwamandan Iran, Qassem Soleimani da Amurka ta yi ranar Alhamis da ta gabata.
Sufeto Janar Muhammad Adamu ne ya bada umarnin yin shirin, a wata takarda da kakakin yada labarai na rundunar, Frank Mba ya sawa hannu kuma ya fitar a jiya Lahadi a hedikawatar rundunar ta kasa da ke Abuja.
“Sufeto Janar ya bada umarni ga dukkan shugabannin sassan ‘yan sanda su sa jami’an da ke karkashin su rika zama da kwana da shirin ko-ta-kwana.
“Sannan kuma su tabbatar da sun samar da cikakken tsaro ga dukkan ofisoshin jakadancin kasashen waje da ke cikin kasar nan, da kuma tsare dukkan wasu muhimman dukiyayi da kadarorin gwamnatin tarayya.”
Haka sanarwar ke dauke, kamar yadda Mba ya fitar ga manema labarai jiya Lahadi.
A cikin sanarwar, Adamu ya jaddada tabbatar da tsaron dukiyoyi da rayukan ‘yan Najeriya, tare da yi musu barka da dawowa daga hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara.
Amurka ta ce ta kashe Soleimani saboda hannun da ya ke da shi wajen kashe wasu Amurkawa, zargin da Iran ta ce karya ce, kuma borin-kunya ne, amma za ta yi ramuwar-gayya.
Tun daga ranar Juma’a ake ta yin Allah-wadai da zanga-zanga a kasashen Musulmi, musamman a Gabas ta Tsakiya.
A Abuja babban birnin Najeriya ma mabiya Shi’a sun gudanar da zanga-zangar la’antar Amurka a ranar Juma’a.
Da dama na ganin cewa wannan ne dalilin da ya sa Sufeto Janar na ‘yan sanda, ya fitar da sanarwar umartar jami’an sa a fadin kasar nan, cewa su daura damarar ko-ta-kwana.
Sai dai kuma ya zuwa yanzu jami’an tsaron ba su ce akwai wata barazana da suka hango ba.