Wani soja da aka ba umarni ya tafi gida neman magani, ya falle zandamemiyar wuka ya kashe mutane biyu, tare da ji wa wasu da dama rauni.
Sojan mai suna Olodi Blessed, da ke Barikin Aikin Injiniya na 401 da ke Jihar Osun, ya kashe wani makwaucin sa da kuma soja data.
Al’amarin ya faru ne cikin barikin sojojin, a ranar 2 Ga Janairu, inda bayan kisan da ya yi kuma ya ji wa matar sa da wasu mutane hudu mummunan rauni da wukar.
Cikin wadanda ya ji wa raunin, baya ga matar sa har da wani soja mai mukamin Lance Kofur. Sai dai kuma sanarwar da ta ce dukkan wadanda aka ji wa raunin su na samun kulawa sosai a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Obafemi Owolowo.
Wadanda ya kashe din dai kamar yadda aka bayyana, an gano cewa akwai wata mata makwauciyar sa mai suna Mrs. Iyabo sai kuma Kofur na soja, wadanda aka ce a yanzu gawarwakin su na can ajiye a dakin ajeye gawarwaki da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Obafemi Owolowo.
Lance Kofur din da aka ji wa rauni na daya daga cikin mutanen da suka yi kumumuwar kokarin kwace wukar a hannun Blessed. Haka wata majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES.
An ce ya yi amfani da wukar ya rika yankan mutane da misalin karfe 9:00 na dare, a ranar 2 Ga Janairu.
Daga nan sai aka kulle shi, bayan da wasu zaratan sojoji suka damke shi, a karkashin jagorancin wani Laftanar.
Majiya a cikin sojoji ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa an tura sojan gida ne daga sansanin fada da Boko Haram a Arewa maso Gabas.
Kakakin yada labarai na Sojojin Najeriya Dibijin na 2, da ke Ibadan, inda can ne wurin aikin Blessed, bai dauki wayar da aka buga masa ba, ballantana a ji karin bayani daga bakin sa.
Fargaba
Duk da dai babu takamaimen irin rashin lafiyar da ta kai Blessed ga aika wannan mummunan kisa, abin da ya faru ya haifar da fargabar halin da sojojin da ke bakin daga da kuma iyalan su ke ciki.
A na juyayin cewa wasu sojojin kan samu tabuwar kwakwalwa a wurin da suke fafata yaki, musamman jin cewa akwai wadanda akan tura tsawon shekaru hudu a wurin, ba tare da an canja ko an sauya suba.
Sai dai kuma mahukunta soja sun sha musanta cewa wannan na da nasaba da tuburewa ko kwarkwancewar wani soja.
An tabbatar da cewa da yawan sojoji sun kashe kan su da kan su, wasu lokuta kuma wasu sai sun kashe wasu sannan su kashe kan su, tun daga lokacin da yaki da Boko Haram ya yi kamari sosai daga cikin 2013.
Discussion about this post