Tsohon gwamnan jihar Barno Kashim Shetimma ya bayyana cewa da so samu ne ya na kaunar ace shima yana cikin makusantar Buhari na kud-da-kud wato ‘Cabal’.
” Ni mutum ne mai son mulki. Yanzu da na dawo garin Abuja a matsayin Sanata, ina tabbatar muku da cewa zan so ace ni ma ina tare da makusantar Buhari na Kud-da-Kud wato ‘Cabal’.
Shettima ya fadi haka ne a wajen taron tattaunawa na shekara-shekara da jaridar Daily Trust ke yi a Abuja.
” Ba a Najeriya ba kawai duk duniya akwai irin wadannan makusanta na shugaban kasa wanda suke tare suna bashi shawarwari. Shugabannin kasar Amurka duk suna da irin wannan makusanta na kud-da-kud.
Ya kara da cewa bai ga wani abin cece-kuce ba da mutane ke yi kan irin wannan makusanta da ke tare da shugaban kasa.
Idan ba’a manta ba ko uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta rika fitowa akai-akai tana yin suka ga wadanda ke tare da shugaban kasa na kud-da-kud.
Irin wannan suka bai tsaya ga makusantar shugaba Buhari ba, abin ya kai ga har dan uwansa Mamman Daura ma bai tsira daga sukar Aisha ba.
Ba ya ga ita ‘yan Najeriya da dama suna yawan koka wa ga wadannan makusantar shugaban kasa suna masu cewa wadannan makusanta sun yi babakere a fadatar gwamnati sai yadda suke so shugaba Buhari ya ke yi.