GWAMNAN IMO: Jigajigan PDP za su gudanar da zanga-zanga a Abuja

0

A dalilin hukuncin kotun koli da ta tsige gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha na jam’iyyar PDP, jigajigan PDP sun yi kurin cewa ba za su amince da wannan hukunci wai an nuna musu karfin gwamnati ne.

Idan ba a manta ba kotun koli ta tumbuke gwamna mai ci na jihar Imo, wato Ihedioha na PDP ta baiwa Hope Uzodinma na APC kujerar gwamnan jihar.

Hope shine ya zo na hudu a wannan zabe.

A jawabin da yayi a wajen taron gaggawa da jam’iyyar ta yi ranar Alhamis a Abuja, shugaban jam’iyyar Uche Secondus ya ce a karkashin shugabancin Tanko Muhammad Kotun Koli ta zubar da kimar ta, babu wata sauran martaba da daraja a kotun, domin Tanko ya damalmala mata lissafi, ya koma ya na kafa wata ajanda ta jam’iyyar APC mai mulki.

“Ai rainin hankali ne ma da kokarin haifar da tarzoma, a ce a kwace mulkin jihar daga hannun mai kuri’u 276,404, a damka ga wanda ya samu kuri’u 96,458, ta hanyar kirkiro wasu kuri’u na gangan, na bogi a dumbuza masa don kawai ana so a damka mulki a hanun sa. To mu ba za mu yarda da wannan rainin wayau din ba.”

“Wannan hukunci da Kotun Koli ta yanke, fashi ne, kuma juyin mulki ne aka yi wa PDP a jihar Imo da ma ’yan Najeriya gaba daya. Don haka bai kamata irin wannan rashin kunyar a bari ta samu wurin zama a karkashin mulkin dimokradiyya ba.”

Tambayoyin Da Secondus Ke So Tanko Ya Amsa

1. Shaidu nawa Uzodinma da APC suka gabatar daga rumfuna 388 din da Kotun Koli ta kamfato kuri’u ta dankara wa masa?

2. Kotun Daukaka Kara da Kotun Sauraren Kararrakin Zabe duk sun yi fatali da tulin katin kuri’un da aka gabatar musu. Ba su ma bude bugunan Ghana Must Go din takardun ba, domin sun ce babu bukatar yin haka. Abin mamaki ne yaushe Kotun Koli ta bude buhunnan har ta kidaya kuri’un da ta kara wa Uzodinma?

3. INEC ta bayar da dalilan da ya sa ba ta gabatar da sakamakon zabukan rumfukan 388 ba.

4. Da yawan wasu rumfunan daga cikin 388 ba a ma yi zabe a wuraren ba. To ina Kotun Koli ta samu yawan kuri’un da ta zabga wa Uzodinma na APC?

Ya aka yi sauran ’yan takara duk basu ma san yawan kuri’un da suka samu a rumfuna 388 ba, sai APC kadai?

Cikin hujjojin da PDP ta kara bayyanawa, har da mamakin yadda aka yi APC da ta kasa cin ko da kujerar majalisar dokoki daya daga cikin kananan hukumomi 27, a ce kuma ta zarce PDP yawan kuri’u a abin da Secondus ya kira makahon hukuncin Kotun Koli a karkashin shugabancin Tanko Muhammad.

Share.

game da Author