Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II Allah Ne Madogarar Sa, Daga Imam Murtadha Muhammad

0

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai

Dukkan godiya da kyakkyawan yabo sun tabbata ga Allah. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabi Muhammad (SAW), da Iyalan sa da Sahabban sa baki daya.

Allah Mai girma! Tsarki ya tabbata ga Allah, mai kowa mai komai. Mai kashe wa, mai raya wa. Mai daukaka wa kuma kaskanta wanda yaso. Mai bayar da mulki, kuma ya kwace mulki daga wanda yaso.

Ya ku jama’a, don Allah ku kalli yadda wasu mutane suke kokarin hada kawunan su da Allah! Sai kace sune masu bayar da mulki da karbe wa ba Allah ba! Ya Allah ka nuna masu kai baka da tamka ko mataimaki, kuma ka nuna masu kai ba azzalumi bane, kuma baka bari ayi zalunci, amin.

Murtadha Gusau

Murtadha Gusau

Jiya Alhamis ne, ranar 16/01/2020, mataimaki na musamman (wato SA) ga gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ta bangaren yada labarai, mai suna Salihu Tanko Yakasai, ya shiga kafafen yada labaran Jihar Kano yayi wasu maganganu na awa daya, aka yada su, kowa yaji shi. Yaci mutuncin Mai Martaba Sarki, yaci mutuncin masarautar Kano mai dimbin tarihi, mai daraja, mai albarka. Ya fadi iya maganganun da yake so na batanci, don ya farantawa mai gidan sa rai.

Cikin maganganun sa yake cewa, wai sun dauki alkawari, kuma sun sha alwashin cewa in dai har sunyi nasara a hukuncin kotun koli da za’a yanke jibi ranar litinin, to ba zasu taba kyale Mai Martaba Sarki akan karagar sarautar Kano ba, sai sun sauke shi! Ga maganar da yayi a takaice:

“Mu a matsayin mu na gwamnati, ba zamu taba yafe wa wannan mutum ba, ba zamu taba hakura ba. Domin shine ya jawo muna dukkan bakin jinin da muka samu kan mu a ciki. A cikin Jihar Kano da wajen Jihar, mutane basa girmama gwamnan mu, basa ganin girman sa, saboda wannan akun Sarkin surutu! Zamu kawo karshen sarautar tasa, in yaso mu ga yaya zai yi shi da magoya bayan nasa! Wannan Sarkin cikin birnin yana ganin cewa yana da goyon bayan jama’ah a duniya, to mu kuma zamu nuna masa muna da karfi da zarar mun ci nasara a kotu!”

Wannan fa ya ku ‘yan uwa masu girma, kadan ke nan daga cikin maganganun da wannan mutum yayi na cin mutunci da batanci ga Mai Martaba Sarki, da kafatanin masarautar Kano, da Kanawa baki daya.

Tun da aka fara rikicin nan, mutanen nan basu da aiki koda yaushe illa cin mutuncin wannan bawan Allah mai daraja.

Su zage shi, suyi masa sharri, suyi masa kazafi, su ce yayi abu alhali bai yi ba, suce yace alhali bai ce ba, idan ya fadi magana su canza ko su juya ta, ko kuma suyi mata mummunar fassara, duk don kawai su bata masa suna, amma saboda Allah Subhanahu wa Ta’ala yayi shi mai hakuri, babu abunda yake ce masu.

Sannan har kullun su ganin suke yi, bakin jinin da suke da shi Mai Martaba Sarki ne ya jawo masu shi, alhali kuwa ba haka bane wallahi. In ban da hauka da rashin hankali irin nasu, ya za’a yi ba zaku yi bakin jini ba? Kun taba tushen addinin mutane da al’adunsu masu kyawo da tarihin su na wurin shekaru dubu, kuna neman ku tarwatsa su, kuyi masu tonon silili, ku raba kan al’ummah, bayan kun tarar da su kawunan su a hade, sannan kuce ba zaku yi bakin jini ba? An gaya maku wannan abun da kuka yi, na rusawa da ruguzawa da tarwatsa masarautar Kano mai dimbin tarihi, karamin laifi ne? Sannan manyan mutane daban-daban, dattijai, shehunnai, malaman addini, sarakuna, ‘yan siyasa, maza da mata masu kima da daraja, masana masu ilimi, ‘yan kasuwa, duk sun ja kunnen ku akan wannan aika-aika da kuke son yi na cin mutuncin masu mutunci, sun gaya maku gaskiya, sun baku shawara ta gaskiya akan ku hakura, ku janye wannan kuduri naku, amma kun yi biris, kun yi kunnen uwar shegu da su, to ku fada mani, don Allah ta yaya ba zaku yi bakin jini ba? Ai wallahi bakin jini kadan ma kenan. Sai kun kasance ma baku kan mulki, a lokacin ne zaku san meye ake kira bakin jini!

Mai Martaba Sarki sam wallahi bai dogara da komai ba in ba Allah ba. Ya san da cewa Allah ne ke yin komai. Mai Martaba Sarki mutum ne da a gaban sa ba boka, ba Dan bori, kuma ba tsafi. Allah ne gatan sa, kuma shine mai yi masa komai. Kuma duk wannan farin jini, da daukaka, da daraja da kuke gani a wurin sa, Allah Subhanahu wa Ta’ala ne ya bashi shi, saboda Allah ya hangi zuciyar sa yaga bata dauke da komai na sharri sai alkhairi ga kowa da kowa. Don haka Allah ya mallaka masa jama’ah a ciki da wajen Jihar Kano. Kuma da ikon Allah, wannan daukaka ta Mai Martaba Sarki, sai dai abunda yayi gaba da izinin Allah.

An zo an gaya wa Annabi Muhammad (SAW) cewa, ga makiya can sun taru a kan ku, sun sha alwashin ganin bayan ku, sai Annabi (SAW) yace, HASBUNALLAHU WA NI’MAL WAKIL. Haka Annabin Allah Ibrahim (AS), makiyan sa sun jefa shi cikin wuta da ransa, da nufin su halaka shi su huta da shi, sai shima ya karanta, HASBUNALLAHU WA NI’MAL WAKIL. Haka muma masoyan mai Martaba Sarki bamu da abunda ya wuce Allah. Don haka mu shine madogarar mu, kuma wallahi ya ishe mu.

Duk wanda yake kuma ganin shi yafi karfin Allah, ko kuma yake ganin kamar shine Allah, ko kuma yake ganin zai iya dora wanda yake so kan mulki, kuma ya sauke wanda yake so, mu ba abun da zamu ce da shi illa, GA SHI GA ALLAH DIN. Zamu gani, da shi da Allah wane ne yafi karfin wani!!!

Kuma mu har kullun, muna kira ga irin wadannan ‘yan siyasar, cewa su gyara dabi’un da halayen su, kuma suyi kokari su gyara mu’amalar su da jama’ah, da kuma mu’amalar su da talakawansu. Domin duk wannan bakin jinin da suke ganin suna da shi, wallahi sune suka jawo wa kan su shi. Idan kuma sun gyara, to sai Allah yasa mutane su kaunace su.

Daga karshe, ina mai mika dimbin godiya ta ga dukkanin Kanawa, da dukkanin ‘yan arewa, da dukkanin ‘yan Najeriya, saboda irin so da kauna da kuke nunawa mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II. Babu abunda zamu ce da ku illa Addu’ar Allah yasa ku gama lafiya, ku da iyalan ku duka. Kuma Allah ya biya maku bukatun ku duniya da lahira. Allah ya kare ku daga dukkan sharri da fitina, amin.

Kuma don Allah muna rokon ku, da kuci gaba da nuna soyayyar ku da kaunar ku ga mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II. Allah ne kadai zai biya ku, kuma yayi maku sakayya duniya da lahira In Shaa Allah.

Shi kuma mai Martaba Sarki, ina rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala da yaci gaba da kare muna kujerar sa, mutuncin sa, da Martabar sa, da imanin sa, amin.

Wassalamu Alaikum,

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a wannan lambar waya kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author