RAMUWAR GAYYA: Iran ta kai wa sansanonin Amurka hari da makaman linzami 15

0

Da jijjifin asubahin yau Lahadi ne sojojin Iran suka kai wa sansani biyu na dakarun Amurka da ke cikin Iraqi hari da makamai masu linzami.
Wannan shi ne hari na farko da Iran ta kai wa sojojin Amurka, tun bayan kisan Janar Soleimani da Amurka ta yi.

Dama Iran ta ce ko tantama babu sai ta rama abin da aka yi mata.

An bada rahoton cewa an kai harin ne da makaman linzami sama da 12 a sansanin sojojin saman Amurka da ke al-Asad da kuma Erbil cikin Iraqi.

Duk da cewa Amurka ta yi gaggawar cewa ba a yi mata barna sosai ba, domin sun gargadi kowa ya fice a guje kafin makaman su fara dira.

Amma kuma gidan talbijin na CNN da kuma kamar yadda Trump ya wallafa a shafin san a tweeter, ya ruwaito Shugaban Amurka Domald Trump na cewa, “To Iran dai ta kai wa sansani biyu na sojojin mu da ke Iraqi hari da makamai masu linzami. Ana nan ana tantance matattu, wadanda suka ji rauni gane irin munin da barnar ta yi mana. Mu duk duniya ba za a nuna mana karfin makamai ba. Shikenan dai, zan yi magana gobe.”

‘Mun Kashe ‘Yan Ta’addar Amurka 80’-Iran

Gidan Talbijin na Iran ya bayyana daya daga cikin shugabannin sojojin kasar na cewa sun sojojin Amurka 80, wadanda ya kira ‘yan ta’adda, a harin da Iran ta kai na ramuwar gayya a sansanonin Amurka biyu da ke Iraqi.

‘Amurkawa su kauce daga bin Tekun Fasha’ –Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi Amurkawa su daina bi ta Tekun Fasha a kan jiragen sama ko a kan jiragen ruwa.
Hakan ya biyo bayan harin ramuwar gayya da Iran ta fara kaiwa sojojin Amurka.

A tekun Fasha dai Amurka ce da Iran suka fi sauran kasashen duniya girka dakarun su tsawo shaekaru masu yawa.

Ana tsoron kuma a can ne yakin Amurka da Iran zai fi muni, idan har ta kai ga an fara yin fito-na-fito.

A yanzu duniya ana ta kiraye-kirayen a tasagaita wuta haka nan.

Idan za a tuna, Dan Majalisa Abolfazi Abuturabi ya bayyana cewa Irann za ta iya kai hari har cikin Fadar White House, fadar Shugaban Amurka Donald Trump.

Wanda ya shirya gangamin taron jana’izar Soleimani, ya yi kiran kowane Ba’Irane ya bada gudummawar dala milyan daya, domin a tara dala milyan 80, wadda za a bai wa duk wanda ya kashe Donald Trump murus.

Majalisar Kasar Iraqi kuma a zaman ta na jiya Lahadi ta kada kuri’ar amincewa da korar sojojin Amurka 5,000 da ke cikin kasar.

Share.

game da Author