Ministar Harkokin Mata Pauline Tallen, ta nada ‘yar ta mai suna Violet Osunde Mai Taimakawa ta Musamman ga Minista.
Ba a kai ga tantancewa shin ta karya dokar aiki, ko kuwa haramtaccen nadi ne Tallen ta yi wa ‘yar ta ba.
Sai dai masu adawa da kungiyoyi da dama na ganin cewa ministar ta nuna son kai da son zuciya, ganin ta rasa wanda za ta dauka duk fadin kasar nan, sai ‘yar cikin ta.
Kafin a dauke ta aiki a ofishin mahaifiyar ta, Osunde na aiki ne a Hukumar Kudaden Fansho ta Kasa, inda aka dauke ta tun cikin 2016. Ta yi aiki a bangaren tattara bayanai na kididdigar alkaluman kudade a hukumar.
‘Yar ta Pauline Tallen dai ta gama digirin ta na farko ne a Jami’ar Plymouth, ta Ingila cikin 2010.
Sai dai kuma da aka tuntubi ministar ta hannun babbar sakatariyar ta mai suna Ms Anagbogu, ta ce ta na da damar daukar duk wadda ta ga dama ko ta ga cewa za ta iya yi mata aikin da ya cancanta a yi domin a kai ga samun nasara.
Amma kuma ta yi bayanin cewa ‘yar ce da kan ta ta nemi a kawo ta ma’aikatar, a matsayin za ta yi aikin bai wa kai hutu na shekara hudu a wurin.
Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta ga takardar sanar da ayyukan da aka bijinta wa Osunde a ofishin mahaifiyar ta. Takardar mai lamba: FMSASW/PS/128/Vol II/302, ta na dauke da bayanan daukar ta aiki da kuma ayyukan da aka dora mata za ta rika yi a ma’aikatar.
Ayyukan sun hada da yin zirga-zirga, karakaina da duk wasu tafiye-tafiye tare da Minista. Watau duk gari ko kasar da mahaifiyar ta za ta tafi, tare za su rankaya.
Tuni dai ta fara aikin ta gadan-gadan, an bar masu adawa na ta hayaniya, ita dai minista ta yi kunnen-uwar-shegu daga dukkan korafe-korafen da ake yi.
Discussion about this post