Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa daga yanzu Najeriya za ta maida hankali wajen tanadar isassun kudaden da za a bukata wajen yi wa yara kanana allurar rigakafi a kasar nan.
Buhari ya fadi haka ne a lokacin da kamfanin sarafa magungunan rigakafi wato GAVI ta kawo masa ziyara a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Ya kuma tabbatar cewa Najeriya ta dauki matakan da za su taimaka wajen samar da kudade da isassun magungunan rigakafi domin yara kanana a kasar daga yanzu har zuwa 2028.
Buhari ya kuma jinjina wa irin goyon bayan da kamfanin GAVI ta ke yi tun daga 2001 musamman a bangaren samar da isassun magungunan rigakafi wa miliyoyin mutane a kasan.
“Rikici da rashin tanada kudaden da ya kamata na daga cikin matsalolin da suka hana kasar nan cimma burinta na inganta yin allurar rigakafi kafin 2021. A dalilin haka kamfanin Gavi ta amince ta ci gaba da tallafa wa kasar nan daga shekaran 2021 zuwa 2028.
Jagorar tawagar kamfanin Gavi kuma shugaban kamfanin Seth Berkeley ya yaba hadin kan da kamfanin ta samu daga wajen gwamnatin Najeriya musamman daga shekaran 2016 zuwa yanzu.
Berkeley ya ce a dalilin haka kamfanin ta shirye domin ci gaba da tallafawa Najeriya daga yanzu har zuwa shekaran 2028.
Ya kuma yi kira ga sauran sassan gwamnati da su tanadi kudade domin samar da isassun magungunan rigakafi a kasar nan.
Idan ba a manta ba kamfanin GAVI ta fara tallafa wa Najeriya da magungunan rigakafi da inganta aiyukkan fannin kiwon lafiya tun a shekaran 2001.
A lissafe Najeriya ta samu wannan tallafi daga wajen GAVI na tsawon shekaru Goma.
Sai dai kuma a ‘yan shekarun da suka gabata GAVI ta yanke shawaran dauke wannan tallafi da Najeriya ke samu ganin ci gaban da kasan ta sumu.
Najeriya ta roki alfarman kamfani da ta ci gaba da tallafa mata kafin kasar ta samu karfin gwiwar kula da kanta. A dalilin haka kamfanin ta amince ta ci gaba da tallafa wa Najeriya na tsawon shekaru Goma.
Shugaba hukumar cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta kasa (NPHCDA) Faisal Shu’aib y ace lalle Najeriya ta samu nasarori da dama wajen yi wa yara allurar rigakafi.
Ya ce bincike ya nuna cewa ci gaban da kasan ta samu ya karu daga kashi 50 a shekaran 2015 zuwa kashi 57 a shekaran 2018.
Duk da haka bincike ya nuna cewa har yanzu yara kanana da dama na rasa rayukansu a dalilin kamuwa da cututtukan da allurar rigakafi zai iya karewa.
Wadannan cututtuka kuwa sun hada da shan inna,bakon dauro,sankarau da shawara.