Hukumar kwastam ta dauki wasu tsauraran matakai domin dakile yaduwar cutar huhu dake kama dabobbi wato ‘Charcoal Anthrax’.
Kwastam ta dauki wannan mataki ne bayan rahotan bullowar cutar a kasar Nijar da ta jiyo daga ma’aikatar kiwon dabobbi da aiyukkan noma ta Najeriya.
Bisa ga rahoton an fara samun bullowar cutar ‘Charcoal Anthrax’ a kasar Nijar ne ranar 23 watan Satumba inda a dan lokaci kadan dabbobi 100 ne suka kamu da cutar sannan 22 suka mutu.
A dalilin haka mataimakin hukumar V.D, Dimka ya bada umurni wa duk ma’aikatan hukumar dake aiki a iyakokkin kasar nan da su sa ido don hana shigowa da dabobbin dake dauke da wannan cuta kasar nan.
Likitocin dabobi sun bayyana cewa kwayoyin cutar ‘Bacteria’ da ake shaka ta iska ne ke haddasa wannan cuta sannan cutar na yin lahani ga fata, huhu da hanjin dabobbi.
Likitocin sun ce shanu,tumakai, jakai da dawakai na daga cikin dabobbin da suka fi kamuwa da wannan cuta.
Likitocin sun bayyana cewa cin naman dabar da ke dauke da cutar, yawan kusantar dabbobi da kashin dabobbin dake dauke da cutar na daga cikin hanyoyin da mutum zai iya kamuwa da cutar.
Sai dai kuma wani babban likitan dabobbi a Najeriya mai suna Olaniyan Alabi ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa cutar bata bullo ba a Najeriya.